Mun Shirya Zamu Fara Tallata Tinubu/Shettima Ga Yan Najeriya, Lalong
- Gwamna Jihar Filato, Simon Lalong, ya ce shiri ya yi nisa na fara yakin neman zaɓen Tinubu da Shettima a zaɓen 2023
- Gwamnan wanda shi ne Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen, ya gana da Bola Tinubu da kakakin majalisar wakilai a Abuja
- Jam'iyyar APC ta naɗa gwamnan a matsayin Daraktan Kanfen ɗin ɗan takararta na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress APC ta bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na fara yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettimi a zaɓen shugaban kasa na 2023 da ke tafe, kamar yadda Punch ta ruwaito
Gwamnan Filato kuma Darakta Janar na yakin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Simon Lalong, shi ne ya yi wannan furucin bayan duba Hedkwatar Kanfen a Abuja.
Kakakin Gwamnan, Dakta Makut Macham, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Jos, ya ce Sakataren Kanfen ɗin APC, Mista James Faleke, ne ya tarbi Lalong a Hedkwatar.
Hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto Macham na cewa Daraktan Kamfen ɗin ya kuma gana da wasu mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen a wani yunkuri na haɗa tawaga mai karfi don fuskantar kanfen.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lalong Ya gana da Tinubu
Bayan haka, a rahoton jaridar Daily Trust, kakakin gwamnan ya ce:
"DG ya yi ganawar sirri da ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a Hedkwatar kamfen."
"Bayan haka kuma mutanen biyu sun shiga wani taron na daban da kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Femi Gbajabiamila da wasu yan majalisu daga majalisar dokokin jihohi."
A wani labarin kuma Gwamnan Adamawa zai jagoranci tawagar Atiku da zata sulhunta rikicin ɗan takarar da gwamna Wike
Ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa gwamnan Adamawa a matsayin shugaban tawagar sulhu da Wike.
Ahmadu Fintiri, ya tabbatar da cewa kafin babban zaɓen 2023 komai zama tarihi a rikicin Atiku da gwamna Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng