Ba Wani Abun Damuwa Idan Peter Obi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Kasa a 2023, Akeredelu

Ba Wani Abun Damuwa Idan Peter Obi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Kasa a 2023, Akeredelu

  • Gwamnan Ondo na jam'iyyar APC mai mulki ya ce ko Peter Obi ya lashe zaɓen 2023 a wurinsa babu wani abun damuwa
  • Gwamna Rotimi Akeredolu ya jima yana jaddada cewa wajibi mulkin Najeriya ya koma kudanci a zaɓen 2023
  • Tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, na APC da Obi na jam'iyyar LP duk sun fito ne daga yankin kudancin Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce ba zai nuna wata damuwa ba idan ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Akeredolu, ya bayyana haka ne a wata hira da kafar Talabijin ɗin Channels TV ranar Laraba, 10 ga watan Agusta, 2022.

Akeredolu, wanda mamba ne a jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku da Tinubu Sun Gamu da Cikas, Wasu Jiga-Jigan APC da PDP Sun Sauya Sheka A Jiha Ɗaya

Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.
Ba Wani Abun Damuwa Idan Peter Obi Ya Lashe Zaɓen Shugaban Kasa a 2023, Akeredelu Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Tinubu da Obi sun fito ne daga yankin kudancin Najeriya yayin da a wurare daban-daban gwamna Akeredolu ya jaddada cewa wajibi mulki ya koma kudu tun da shugaba Buhari, wanda wa'adinsa zai kare a 2023, ɗan arewa ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wane Ɗan takarar gwamnan ke goyon baya?

Da aka tambaye shi ko zai goyi bayan takarar Musulmi da Musulmi idan da yana tsagin hamayya, Gwamnan Ondo ya ce bai kamata a tsaya ana kace-nace kan addini a zaɓen 2023 ba.

The Cable ta rahoto gwamnan na cewa:

"Na faɗi makamancin haka idan kun saurari lakcata yau, na yi bayani a fili, addini ba abun ɗaga hankali bane yanzu. Muna da sauran batutuwan da suke a sahun gaba, batun sake fasalin ƙasa, mulkin karɓa-karɓa da sauran su."
"Tun 1999, akwai yarjejeniyar cewa zamu rinƙa karɓa-karba daga arewa zuwa kudu, idan yau an samu wasu da ke kokarin cusa abinda ni na kira da yaudarar mutane da addini da tunanin canza karɓa-karɓa, to ba zamu yarda ba."

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Shugaban APC Na Ƙasa Ya Magantu Kan Shirin Majalisa Na Tsige Shugaba Buhari

"Ni a wuri na, ba wai don saboda Asiwaju Bola Tinubu ba, idan ka saurari lakca ta, na faɗi cewa idan Peter Obi aka zaɓa shugaban kasa, hakan ya mun daidai, idan Tinubu aka zaɓa dai-dai ne. Ni fa kawai dole ya koma kudu."

A wani labarin kuma Kokarin ɗinke barakar PDPya gamu da cikas, Shugabar Mata da daruruwan mambobi sun koma APC

Jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta kara karfi tare da sauya sheƙar wasu ɗaruruwa mambobin PDP a shiyyar Kebbi ta tsakiya.

Shugabar Matan PDP ta shiyyar, Yar Sakkwato Jega, tare da wasu ɗaruruwan masoyanta sun rungumi tsintsiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262