Wasu Jiga-Jigan APC da PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo

Wasu Jiga-Jigan APC da PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo

  • Ɗan takarar jam'iyyar Accord Party, Adebayo Adelabu ya samu ƙarin goyon baya na wasu manyan yan siyasa a Oyo
  • Wasu jiga-jigan APC da PDP tare da dumbin magoya bayan su sun bi sawun Adelabu zuwa Accord don ganin ya zama gwamna a 2023
  • Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Adelabu, ya koma Accord ne domin cika burinsa na zama gwamna

Oyo - Ɗan takarar gwamnan Oyo karkashin inuwar jam'iyyar Accord Party a 2023, Adebayo Adelabu, ya samu gagarumin goyon bayan a shirinsa na lashe zaben 2023.

Premium Times ta rahoto cewa jigon jam'iyyar APC, Adegboyega Adegoke, da wani jigon jam'iyyar PDP, Fatai Adesina, sun bi sahun ɗan takarar, inda suka sauya sheka zuwa Accord Party (AP).

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

Adebayo Adelabu.
Wasu Jiga-Jigan APC da PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mai taimakawa Mista Adelabu ta fannin kafafen watsa labarai, Femi Awogboro, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ya bayyana cewa manyan yan siyasan biyu sun yanke komawa jam'iyyar AP ne domin tabbbatar da Mista Adelabu ya lashe zabe mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta gano cewa Adelabu, wanda ya fi shahara da sunan Penkelemesi, ya rike kujerar mataimakain gwamnan babban bankin Najeriya CBN a baya.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa Mista Adegoke ya nemi tikitin takarar Sanatan Oyo ta kudu, yayin da Adesina ya kasance tsohon mamba a majalisar dokokin jiha.

Awogboro ya ce:

"Kwarai kuwa, sun shigo gida ne baki ɗayansu, Adegoke, shugaban gidan Radiyon Solution FM ya nemi takarar Sanatan Oyo ta kudu a zaɓen fidda gwanin APC. Adesina ya lashe zaɓen mamba a majalisa dokokin jiha a 2015."

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Samu Babban Tawaya A Yayinda Fitaccen Jigonta Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar

"Tawagar yaƙin neman zaɓen Adelabu na ƙara karfi, goyon bayan da muke samu musamman a yan makwannin nan alama ce dake nuna cewa jam'iyyar Accord ce zata ɗaga jihar mu a 2023."

Akwai masu sauya sheƙa nan gaba - Awogboro

Ya ƙara da cewa Jam'iyyarsu zata karɓi karin manyan jiga-jigan PDP da APC a watanni masu zuwa don tabbatar da an kafa gwamnati mai nagarta a Oyo.

A nashi jawabin Adegoke, ya ce ya biyo sawun Adelabu tare da tawagar Magoya bayansa na siyasa da abokanai da ke faɗin jihar Oyo.

A wani labarin kuma Wata Sabuwa a PDP, Wani ɗan majalisar tarayya ya Fallasa jiga-jigan da suka haddasa rikicin Atiku da Wike

Ɗan majalisar tarayya daga jihar Ribas, Solomon Bon, ya yi ikirarin cewa na kusa da Atiku ne suka haddasa rikicin PDP tun farko.

A cewarsa, tun farko sun yaɗa wasu karerayi game da Wike kafin da kuma bayan zaben fidda gwani da nufin rage masa ƙima.

Kara karanta wannan

Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262