DA DUMI-DUMI: APC Ta Bayyana Lalong a Matsayin Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Tinubu

DA DUMI-DUMI: APC Ta Bayyana Lalong a Matsayin Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Tinubu

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da nadin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a matsayin Darakta Janar na yakin neman Zabe Tinubu
  • Jam’iyyar APC ta bayyana karamin ministan kwadago da samar da ayyuka Festus Keyamo a matsayin kakakin rikon kwarya
  • Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya Sanar da Shugaba Buhari da sabin nadin da Jam'iyyar ta yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da nadin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a matsayin darakta-janar na yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Tinubu. Rahoton Leadership

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Adamu ya samu rakiyar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mataimakin dan takarar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da gwamnan jihar Filato, Lalong.

Lalong
DA DUMI-DUMI: APC Ta Bayyana Lalong a Matsayin Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Tinubu
Asali: UGC

Shugaban ya kuma bayyana nadin karamin ministan kwadago da samar da ayyuka Festus Keyamo a matsayin kakakin rikon kwarya kuma mawallafiyar jaridar LEADERSHIP Hannatu Musawa a matsayin mataimakiyar mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

PDP Ta Zargi Zulum da Gina Manyan Makarantu Da Babu Kwararrun Malamai

A wani labari kuma, Dan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Borno, Alhaji Mohammed Jajari, ya soki gwamnatin jihar Borno a karkashin Gwamna Babagana Umara Zulum na gina manyan makarantu a fadin jihar ba tare da kwararrun malamai da za su jagoranci makarantun ba. Rahoton LEADERSHIP

Dan takarar gwamnan a jam’iyyar PDP ya ce duk da rashin isassun malamai a jihar, gwamnati ta fara shirin sallamar wadanda ake da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa