Da Duminsa: Fitaccen Sanatan APC Daga Arewa Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari
- Ana samun karin yan majalisar tarayya da a yanzu ke goyon bayan tsige Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
- Daya daga cikin wadanda ya nuna goyon bayansa kan kirar neman tsige shugaban kasar shine Sanata Elisha Abbo na jam'iyyar APC a ranar Juma'a 29 ga watan Yuli
- A ra'ayin Abbo, Shugaba Buhari ya sauka daga mukaminsa saboda ya gaza tsare rayyuka da dukiyoyin yan Najeriya
Sanata Elisha Abbo, dan majalisar tarayya daga Adamawa North ya goyi bayan kiran da sanatocin jam'iyyun adawa suka yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Abbo ya bayyana matsayinsa ne kan batun tsige shugaban kasar a wurin taron shugabannin kiristoci na Arewa da aka yi a ranar Juma'a 29 ga watan Yuli a birnin tarayya, Abuja.
Sanatan ya fada wa yan jarida cewa dalilinsa na goyon bayan kiran tsige shugaban kasar shine mummunan halin rashin tsaro da ake ciki a kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar dan jaridar, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza wurin sauke nauyin da aka dora mata na farko wato kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.
Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari
A wani labari mai alaka da wannan, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya goyi bayan yunkurin da majalisar dattawa na tsige Shugaba Muhammadu Buhari saboda matsalar tsaro da ke adabar kasar.
A cewar wani rahoto da jaridar ThisDay ta fitar, Gwamna Ortom na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya jinajinawa majalisar tarayyar kan wa'adin sati-shida da ta bawa shugaban kasa.
Gwamna Ortom ya bayyana goyon bayansan ne a masaukinsa da ke Abuja, ranar Juma'a 29 ga watan Yuli yayin tarbar tawagar yan majalisa marasa rinjaye da Sanata Philip Aduda ya yi wa jagoranci.
Asali: Legit.ng