2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na ADC, Kachikwu, Ya Bayyana Buhari A Matsayin Mataimakinsa

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na ADC, Kachikwu, Ya Bayyana Buhari A Matsayin Mataimakinsa

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar ADC, Dumebi Kachikwu, ya bayyana Ahmed Buhari a matsayin abokin takararsa
  • Da yake tsokaci kan halin da ƙasa ke ciki, Kachikwu ya ce idan ADC ta kafa gwamnati zata dawo da zaman lafiya
  • Ahmed Buhari ya ce ya yarda ya zama abokin takara ne saboda burinsa na kawo canji mai kyau a Najeriya

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya bayyana Ahmed Buhari a matsayin abokin takararsa a babban zaɓen 2023.

Leadership ta rahoto cewa Buhari, wanda yake jakadan ƙungiyar Afirka, mutum ne mai nagarta game da jagoranci kuma ya fito ne daga jihar Neja.

Haka zalika, Ahmed Buhari, ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Sustainable National Party of Nigeria yayin babban zaɓen 2019.

Kara karanta wannan

Ana Batun Tsige Shi, Shugaba Buhari Ya Naɗa Surukinsa Da Wasu Mutum Biyu Manyan Muƙamai A Tarayya

Abokin takara, Ahmed Buhari.
2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na ADC, Kachikwu, Ya Bayyana Buhari A Matsayin Mataimakinsa Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Da yake ayyana abokin takararsa a Abuja, Kachikwu, shugaban gidan Talabijin na Root tv, ya caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan yanayin rashin tsaro da Najeriya ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar ADC, wanda ya nemi shugaban kasa ya yi murabus, ya bayyana gwamnatin APC mai mulki da mayaudariya.

A rahoton jaridar Punch, Kachikwu ya ce:

"Jam'iyyar ADC ta zo ta ceci Najeriya, ta tsamo ƙasar nan daga halin taɓarɓarewar tsaro da faɗuwar tattalin arziki da ake fama da su."

Ɗan siyasan ya kuma yi wa yan Najeriya alƙawarin cewa da zaran ADC ta kafa gwamnati, yajin aikin ƙungiyar Malaman Jami'o'i zai zama tarihi a Najeriya.

Yadda zan magance matsalar tsaro - Kachikwu

Da yake tsokaci kan tsaro, ya ce domin daƙile kalubalen da ya zame wa ƙasar nan karfen kafa, zai ɗauki sabbin dakaru a rundunar sojojin Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sanatoci sun yi barazanar tsige shugaba Buhari, sun ba shi wa'adin mako 6

Kachikwu ya ce:

"Yayin da yan ta'adda ke kokarin ɗaukar mayaƙa, su kuma hukumomin tsaro ba su ɗauka. Idan muna son kawo ƙarshen yan ta'adda, wajibi mu ɗauki jami'ai a hukumar sojoji."

A nashi ɓangaren, ɗan takarar mataimaki, Ahmed Buhari, ya ce amincewarsa ta haɗa karfi da Kachikwu da jam'iyyar ADC ya samo asali ne daga burinsa na kawo canji a Najeriya.

A wani labarin kuma Mai bada shawara ka. harkokin tsaro, NSA Babagana Monguno, ya faɗi abubuwan da aka tattauna a taron tsaro da Buhari

Ya ce a yanzu haka gwamnatin ta duƙufa aiki da dare ba rana kan sabbin dabarun da zasu kawo ƙarshen matsalar tsaro baki ɗaya a Najeriya.

A cewarsa, majalisar koli ta tsaro ta amince da wasu sabbin dabaru domin ganin bayan matsalar, ya tabbatar da cewa za'a ƙara matsa kaimi kan ayyukan ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262