Atiku Da Gwamna Okowa Sun Gana Da Sanatocin PDP A Kokarin Rarrashi
- Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya fara koƙarin rarrashin mambobin jam'iyya gabanin zaɓen 2023
- A wani babban yunkuri, Atiku da abokin takararsa sun gana da Sanatocin PDP domin shawo kan waɗan da suka fusata
- Babbar jam'iyyar hamayya ta shiga rikici ne tun bayan kammala zaɓen fidda gwani wanda Atiku ya lashe
Abuja - Mambobin jam'iyyar PDP da ke majalisar dattawan Najeriya sun gana da ɗan takarar jam'iyyarsu na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ɗan takarar mataimaki, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ranar Talata.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an gudanar da taron ne a wani ɓangare na rarrashin mambobin jam'iyya waɗan da suka fusata domin tunkarar babban zaɓen 2023.
Atiku ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa:
"A daren jiya, abokin takara na, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da ni kaina mun gana da Sanatocin jam'iyyar mu karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Manyan jiga-jigan babbar jam'iyyar hamayya kamar irin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, sun nuna ƙarara ba su jin daɗin cigaban da ake samu a PDP.
Gwamna Wike ya sha kaye a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa wanda Atiku Abubakar ya lashe, haka nan kuma an tsallake shi lokacin zaɓo ɗan takarar mataimaki.
Bayan Wike, ɗaya daga cikin masu faɗa aji na PDP, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya nuna damuwarsa kan yadda ake yi wa gwamnan Ribas rashin adalci.
Ortom ya bayyana cewa ya kamata ace an nemi shawararsa kafin ɗaukar matakin zaɓo gwamna Okowa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP.
Zamu rarrashi mambobi - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sha alwashin haɗa kan jam'iyyar gabanin zuwan babban zaɓen 2023.
Daga cikin waɗan da suka halarci taron wanda ya gudana ranar Talata har da shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.
Hotunan taron
A wani labarin kuma kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP Peter Obi ya maida zazzafan martani ga Atiku Abubakar kan zaɓen 2023
Tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ya ƙosa ya ba da mamaki a babban zaɓen 2023.
Peter Obi, yayin martani ga kalaman Atiku Abubakar na PDP, ya ce dama can rayuwar siyasarsa cike take da abubuwan Al'ajabi.
Asali: Legit.ng