Gwamna El-Rufa'i, Matawalle Da Jigon APC Sun Ziyarci Bola Tinubu A Abuja
- Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna da wasu gwamnonin arewa biyu sun ziyarci jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja
- Abokin takarar Tinubu, Sanata Kashin Shettima, Sakataren APC na ƙasa da tsohon shugaba, Oshiomhole sun halarci taron
- Babu wani bayanai kan dalilin ganawar amma ana ganin ba zai rasa alaƙa da shirin tunkarar babban zaɓen 2023 ba
Abuja - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna da Simon Lalong na jihar Filato, sun ziyarci ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a Abuja.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnonin guda uku sun gana da Tinubu da ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Ƙashin Shettima.
Sauran jiga-jigan jam'iyya mai mulki da suka halarcu taron sun haɗa da Sakataren APC na ƙasa, Iyiola Omisore, da tsohon shugaban jam'iyya na ƙasa, kwamaret Adams Oshiomhole.
Duk da ba bu wani cikakken bayani kan abin da suka tattauna, ammma ana ganin ziyarar ba zata rasa nasaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2023 da ke tafe ba.
Hotunan ziyarar jiga-jigan ga Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ziyara na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun nuna cewa wasu gwamnonin cigaba daga yankin arewa ba su ji daɗin matakin Tinubu na zaɓo Shettima ba.
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai na ɗaya daga cikin waɗan da matakin be musu daɗi ba, sai dai Sanata Uba Sani ya musanta rahoton da cewa El-Rufai zai ja ragamar APC ga nasara a 2023.
A wani labarin kuma An bayyana sunaye da cikakken bayanan Sojojin fadar shugaban ƙasa da yan ta'adda suka kashe a Abuja
A jiya Litinin ne wasu yan ta'adda suka mamayi dakarun soji da ke tsaron fadar shugaban ƙasa a yankin Bwari a Abuja.
Harin ya yi sanadin mutuwar jami'ai guda uku, cikakken bayanan wasu daga cikin mamatan sun bayyana mun tattara muku su.
Asali: Legit.ng