Adeleke: A Shirye Na Ke, Mutanen Osun Ba Za Su Yi Nadamar Zabe Na Ba
- Sanata Ademola Adeleke, zababben gwamnan Jihar Osun ya ce a shirye ya ke tsaf ya fara yi wa mutanen jiharsa hidima
- Adeleke ya ce ya san kallubalen da mutanen jiharsa ke fuskanta amma zai mayar da hankali domin ganin sun dara kamar wasu jihohi
- Zababben gwamnan ya yi mutanen Osun alkawarin cewa ba za su yi nadamar zabensa ba domin ya koyi darasi tun shekaru hudu da ya rasa damar zama gwamnan
Jihar Osun - Zababben gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya yi wa mutanen Osun alkawarin cewa ya shirya yi musu hidima.
Ya ce ya san kallubalen da jihar ke fuskanta amma zai yi kokarin magance su ba tare da jin tsoro ba, rahoton The Punch.
Adeleke, wanda shine dan takarar PDP ya doke gwamna mai ci a yanzu kuma dan takarar APC Adegboyega Oyetola, ya lashe zaben na ranar 16 ga watan Yuli.
A cewar hukumar zabe ta INEC, Adeleke ya samu kuri'u 403,371 ya kuma ci zabe a kananan hukumomi 17 ya doke Oyetola, wanda ya samu kuri'u 375,027 ya kuma ci kananan hukumomi 13.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalla kananan hukumomi 15 ne suka yi takara a zaben.
A hirar da ya yi da The Punch a ranar Asabar, Adeleke, wanda ya karbi takardan nasarar cin zabe daga INEC a ranar Laraba ya ce:
"Zabe na da mutanen Osun suka yi daga Allah ne. Na shirya jagoranci. Na kuma san kallubalen da mutanen mu ke fuskanta a jihar mu. Ina son tabbatar maka da mutanen jihar mu ba zan basu kunya ba.
"Zan iya jagorancin jihar kuma zan yi hakan da tsoron Allah. Zan bada jagoranci da ake bukata. Na koyi darrasi sosai cikin shekaru hudu da suka wuce lokacin da aka sace mana nasarar mu.
"Na yi alkawarin ba zan bawa mutane kunya ba. Za mu bada muhimmanci kan bukatun mutane. Mutanen Osun sun wahala, suna bukatar su yi murmushi kamar takwarorin mu da ake aiki. Za mu yi hakan."
INEC ta bawa Ademola Adeleke takardar shaidar nasarar cin zaɓe
Tunda farko, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta mika takardar shaidan nasarar cin zaɓe ga Ademola Adeleke, zabebben gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, rahoton The Cable.
Oyetola yana shirin garzayawa kotu domin kallubalantar nasarar dan takarar na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng