Atiku: Peter Obi Ba Zai Lashe Zaɓen Shugaban ƙasa a 2023 Ba, Kashi 90% Na Yan Arewa Basu Soshiyal Midiya

Atiku: Peter Obi Ba Zai Lashe Zaɓen Shugaban ƙasa a 2023 Ba, Kashi 90% Na Yan Arewa Basu Soshiyal Midiya

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce baya tunanin Peter Obi zai kai labari a babban zaɓen 2023
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce ba ya ganin wani abun aljabi zai faru duba da kashi 90% na mutanen arewa ba su Soshiyal Midiya
  • Atiku ya yi wannan magana ne yayin da ake ta yaɗa cewa jam'iyyar LP zata lakume wasu kuri'u da ya dace PDP ta samu

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce ko kaɗan baya tsammanin jam'iyyar Labour Party zata ba da mamaki ta lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan Talabijin na Arise TV ranar Jumu'a.

Da yake tsokaci kan yuwuwar LP ta lashe zaɓen 2023, Atiku ya ce jam'iyyar Peter Obi ba zata iya raba kuri'un PDP ba kamar yadda wasu ke hasashe.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake rijiya da baya lokacin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya magantu a Kotu

Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku: Peter Obi Ba Zai Lashe Zaɓen Shugaban ƙasa a 2023 Ba, Kashi 90% Na Yan Arewa Basu Soshiyal Midiya Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ɗan takarar PDP ya yi misali da kokarin LP a zaɓen gwamnan Osun da ya kammala, inda ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da gwamnoni, mambobi a majalisun tarayya da majalisun dokoki na jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tha Cable ta rahoto Atiku ya ce:

"Bana tsammanin LP zata rage wa jam'iyyar PDP kuri'u kamar yadda mutane ke zato. Idan muka duba zaɓen gwamnan Osun, me jam'iyyar LP ta taɓuka? Ita ce jam'iyyar da bata da gwamna, mamba a majalisar tarayya da na jihohi."
"Kuma siyasar ƙasar nan ta dogara da abinda kake da shi a kowane mataki, matakin ƙananan hukumomi, matakin jihohi da ƙasa baki ɗaya."

Mafi yawan yan arewa basu Soshiyal midiya - Atiku

Bugu da ƙari, Atiku ya ce kashi 90% na mazauna arewa ba su amfani da kafafen sada zumunta, wata alama da zata rage damarmakin LP na lashe zaɓen a 2023.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

"Saboda haka ya na da wuya ka yi tsammanin wani abun al'ajabi zai faru, saboda kawai Peter Obi ya koma jam'iyyar LP. Bayan haka, suna ta soki burutsun su a soshiyal midiya, suna da ƙuri'u sama da miliyan ɗaya a Osun."
"Amma ya kuri'un suka fito ga LP? Kuma bayan haka, kuna maganar kafafen sada zumunta, kashi 90% na mutanen mu basu damu da soshiyal midiya ba."

A wani labarin kuma Atiku ya bayyana dalilin da yasa bau ɗauki gwamna Wike a matsayin abokin takararsa na 2023 ba

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai zabi Wike a matsayin abokin takararsa ba, saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci.

Atiku Abubakar ya dauki Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262