2023: Ɗan Takarar Gwamnan Legas Ya Karɓi Tawagar Mambobin APC Zuwa PDP

2023: Ɗan Takarar Gwamnan Legas Ya Karɓi Tawagar Mambobin APC Zuwa PDP

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Legas karƙashin inuwar PDP, Dakta Adediran, ya ce ya karbi mambobin APC da suka sauya sheƙa
  • Adediran, wanda ya bayyana sunan tawagar masu sauya shekan, ya ce sun bar APC ne saboda sun yarda da alƙawarin jam'iyyar PDP
  • Tun bayan kammala zaɓen fidda yan takara, jam'iyyar APC ke fama da rikicin cikin gida wanda ke cigaba da ɗibar 'ya'yanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Ɗan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a jihar Legas, Dakta Olajide Adediran, wanda ya fi shahara da Jandor, ya karɓi tawagar masu sauya sheƙa daga jam'iyyar APC.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tawagar masu sauya shekan daga kananan hukumomi 20 da ke faɗin jihar sun koma PDP yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.

Dakta Olajide Adediran.
2023: Ɗan Takarar Gwamnan Legas Ya Karɓi Tawagar Mambobin APC Zuwa PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar ɗan takarar gwamnan, Jandor, ya tarbi mambobin jam'iyyar APC mai mulki zuwa babban jam'iyyar hamayya watau PDP ranar Laraba.

Kara karanta wannan

APC ta sake rashin babban jigo, Tsohon Sanata kuma Ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

A kalamansa, Jandor ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na karɓi wasu mambobin jam'iyyar All Progressive Congress wato APC waɗan da suka watsar da jam'iyyar, suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP."

Meyasa suka ɗauki matakin ficewa daga APC mai mulki?

Ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa masu sauyan shekan sun ce sun yi haka ne saboda yarda da alƙawarin PDP na gyara goben Najeriya.

"Sunan tawagar masu sauya sheƙar 'Best Alternative Network' kuma sun ce sun yanke barin APC ne duk da kasancewarta jam'iyya mai mulki saboda suna da yaƙini kan alƙawarin mu na gina Najeriya da ceto ƙasa daga halin da ta shiga ƙarkashin APC."

A wani labarin kuma Kokarin shawo kan rikicin PDP ya gamu da cikas, Wani Jigo a shiyyar arewa ya fice daga jam'iyyar

Babban jigon PDP kuma ma'aji a reshen shiyyar arewa maso gabas, Abba Itas, ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Ɗan majalisa ya fice daga jam'iyyar APC, ya koma jam'iyyar hamayya

Honorabul Abba ya bayyana cewa ya yi haka ne sakamakon rashin adalci da zaluntar da aka yi wa gwamna Wike na Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262