Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu, Shettima ya fadawa Buhari
- Kashim Shettima ya fadawa shugaba Buhari cewa Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu
- Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ki amincewa da tayin zama abokin takarar Tinubu da gwamnonin APC suka mishi
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayan sa ga kashim Shettima a lokacin da ya kai mishi ziayar a Abuja
Abuja - Kashim Shettima ya fadawa shugaba Buhari cewa Gwamnonin APC sun so Zulum ya zama abokin takarar Tinubu kamar yadda PREMIUM TIMES ta rawaito.
Shettima ya nemi shugaba Buhari ya yiwa Zulum godiya akan yadda ya rika ambaton sunan sa, a duk lokacin da aka masa tayin zama abokin takarar Tinubu.
Amma gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya ki tayin duk da matsin lamba daga takwarorin sa gwamnoni.
Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun matsa wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, lamba da ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC amma yaki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A baya Legit.Ng ta ruwaito cewa Kashim Shettima ya ziyarci Buhari bayan an kaddamar da shi abokin takarar Tinubu a hukumance a ranar Laraba a Abuja.
Mista Shettima ya samu rakiyar Mista Zulum da karamin ministan noma, Mustapha Shehuri.
A taron da aka yi a ranar Laraba, Mista Buhari ya bayyana goyon bayan sa in da ya ce jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023, kuma zai mika wa Tinubu da Shettima karagar mulki a 2023.
Buhari ya gana da Shettima bayan an kaddamar da shi abokin takarar Tinubu
A wani labari kuma, Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya kai wa shugaba Buhari ziyara a fadar gwamnati da ke Abuja bayan an kaddamar dashi abokin takarar Tinubu. Rahoton PUNCH
Gwamnan jihar Borno yana cikin tawagar da suka raka Kashim Shettima fadar shugaban kasar da misalin karfe 04:00 na yammacin ranar Laraba.
Asali: Legit.ng