Yanzu-Yanzu: INEC ta bawa Ademola Adeleke takardar shaidar nasarar cin zaɓe

Yanzu-Yanzu: INEC ta bawa Ademola Adeleke takardar shaidar nasarar cin zaɓe

  • Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta mika takardan shaidan nasarar cin zabe ga Ademola Adeleke, zababben gwamnan Jihar Osun
  • Adeleke, dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya lallasa abokin hamayyarsa kuma gwamna mai ci Gboyega Oyetola inda ya samu kuri'u 403,371
  • A Zaben gwamnan Osun a shekarar 2018, an fafata tsakanin Adeleke da Oyetola amma a wancan lokacin dan takarar ba APC ya yi nasara bayan an yi zaben raba gardama

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta mika takardar shaidan nasarar cin zaɓe ga Ademola Adeleke, zabebben gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, rahoton The Cable.

Ademola Adeleke
Yanzu-Yanzu: INEC ta bawa Ademola Adeleke takardar shaidar nasarar cin zaɓe. Hoto: @davido.
Asali: Facebook

Adeleke ya samu kuri'u 403,371 inda ya doke Gboyega Oyetola, gwamnan Osun kuma ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress APC a zaben na gwamna.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

Oyetola yana shirin garzayawa kotu domin kallubalantar nasarar dan takarar na jam'iyyar PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda Adeleke ya sha kaye hannun Oyetola a shekarar 2018

A shekarar 2018, Dan takarar na jam'iyyar PDP na kan gaba da kuri'u, amma aka ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba saboda adadin kuri'un da aka soke ya fi ratar da ke tsakanin jam'iyyun biyu.

Oyetola, daga bisani ya zama gwamna bayan ya lashe zaben raba gardama. Duk da Adeleke ya tafi kotu don kallubalantar zaben, kotun koli a watan Yulin 2019 ta jaddada nasarar Oyetola.

Rahotanni sun ce rikici tsakanin Oyetola da Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida, wanda shi ke da iko da jam'iyyar a jihar ya taimaka wurin bawa Adeleke damar lashe zaben.

Ministan bai hallarci yakin neman zaben APC a jihar ba kuma bai kada kuri'a a zaben ba, inda hadimansa suka ce ya tafi kasar waje don wakiltar Najeriya a wani taro.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: APC ta dauki Lauyoyi 50 da za su kalubalanci nasarar Adeleke a kotu

Gwamna Oyetola zai kalubalanci sakamakon zaben Osun da lauyoyi 50

A bangare guda, Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola kuma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna da aka kammala a jihar ya shirya tsaf domin kalubalantar zaben a kotu, Rahoton Vanguard.

Da yake magana da Vanguard akan nasarar Adeleke, Kunle Adegoke, babban lauya wanda mamba ne a cikin kungiyar lauyoyin Oyetola ya bayyana cewa lauyoyi 50 ne suka nuna sha’awar shiga shari’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164