INEC zata samar da hukunci na tsawon rayuwa ga duk ɗan siyasa da aka kama da sayen Kuri'u
- Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bukaci a samar da hukuncin haramcin shiga zaɓe na har abada ga duk wanda aka kama da sayen kuri'u
- Kwamishinan INEC na jihar Akwa Ibom, Mike Igini, ya ce ba Najeriya kaɗai haka ke faruwa ba, manyan kasashen duniya sun sha fama da matsalar
- Sai dai ya ba da misalin yadda suka shawo kan matsalar inda ya nemi majalisar tarayya su yi koyi da hakan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Akwa Ibom - Kwamishinan hukumar zaɓe ta ƙasa INEC na jihar Akwa Ibom, Mike Igini, ya nemi a samar da hukuncin haramcin shiga siyasa na tsawon rayuwa ga duk ɗan siyasa ko jam'iyyar da aka kama da sayen kuri'un al'umma.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa batun sayen kuri'u da siyarwa sun ci kasuwa a zaɓen gwamnan Ekiti da ya gudana a watan da ya shuɗe da zaɓen Osun da ya kammala ranar Asabar da ta gabata.
Da yake ba da shawarin samar da hukuncin jiya, Mista Ingi, wanda ya yi jawabi a cikin shirin 'Mornin Rise' na Channels TV, ya ce, "Haɗarin sayen kuri'u ya kai matakin Annoba kuma shi ne babban abun da muke bukatar ganin bayansa."
A kalamansa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sayen ƙuri'u ya zama matsala kuma zai yi babban tasiri idan ba mu dakile shi ba a yanzu. Tasirin sayen kuri'u na farko shi ne zai kawar da siyasar yi wa al'umma aiki saboda yadda abun yake, idan na kan mulki ya yi aiki a zabe na gaba zai girbi sakamakon aikinsa."
"Amma idan ba'a kawar da sayen kuri'u ba, daga nan babu zancen aikin da ka yi saboda abunda mutum zai bukata shi ne kudin sayen kuri'u. Na biyu. idan ba'a dakatar sayen kuri'u ba zai kawo rashin daidaito saboda mulki zai koma hannun masu kuɗi kaɗai."
"Haka nan kuma zai haifar da abun da ake kira tsarin nuna banbanci. Idan muka bar sayan kuri'u ya cigaba da cin karensa babu babbaka, to ba za'a samu daidaito wajen gudanar da ayyuka ga al'umma ba."
Mista Igni ya ƙara da cewa kasashen da suka cigaba kamar su Amurka, Birtaniya da ƙasashen Latin America duk sun sha fama da lamarin sayen kuri'u amma sun ɗauki matakin magance shi.
Haramun ne sayen kuri'a a dokar zaɓe - REC
Haka nan ya ba da misali cewa a Ingila zaka iya amfani da $5000 ka sayi kuri'u 850 daga cikin 1000 amma sai yan majalisun su suka kafa wata doka, "Idan aka kama ka kana sayen kuri'a za'a haramta maka shiga zaɓe na shekara 6."
"Idan ka sake maimaita sayen kuri'u to da kai da jam'iyyarka za'a haramta muku shiga zaɓe har abada."
Kwamishinan INEC ya buƙaci yan majalisun tarayya da su yi koyi wajen kafa irin wannan doka, inda ya ƙara da cewa ba za'a mance da su ba a tarihi idan suka yi haka.
Bugu da ƙari, ya jawo sashin kundin zaɓe da ya haramta saye ko sayarda kuri'a, inda ya ce kuri'a ita ce yancin da ɗan kasa ke da shi.
A wani labarin kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a birnin Shehu ta ce babu ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
Da take yanke hukunci, ta tabbatar da hukuncin farko da babbar Kotun tarayya ta Gusau ta yanke kan gwamna Bello Matawalle.
Asali: Legit.ng