Cocin su Osinbajo ta RCCG ta yi magana akan ganawar sirri da aka yi da Tinubu
- Cocin RCCG ta ce, Fasto Enoch Adeboye bai gana da Bola Ahmed Tinubu akan takarar tikitin Musulmi da Musulmi a zabe mai zuwa
- Cocin RCCG ta ce, ba taba goyon bayan kowani dan takarar kuma baza ta goyi kowa ba a zabe 2023 mai zuwa
- RCCG ta gargadi kafafen yada labarai da su daina yada labaran karya game da Fasto E.A. Adeboye ko ta dauki mataki
Jihar Ogun : Kungiyar Redeemed Christian Church of God, RCCG, ta yi karin haske akan ganawar da aka yi tsakanin babban Faston su, Enoch Adeboye , da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu. Rahoton VANGUARD
RCCG ta ce sabanin rahotanni dake yawo a kafofin yada labaru, Fasto Adeboye bai taba ganawa da Tinubu akan tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi ba.
Wata jarida ta kasa ta ce Tinubu ya gana da Adeboye akan takarar sa a karshen makon da ya gabata.
Sai dai wata sanarwa da cocin ta fitar, ta yi watsi da ikirarin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A sanarwar cocin ta ce:
“Mun samu labarin cewa wasu sabbin kafafen yada labaru sun fitar da rahoton dake nuna Fasto E.A. Adeboye, ya gana da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu akan takarar sa kuma yana goyon bayan sa.
“Ya kamata kafafen yada labarai su daina yada labaran karya game da Fasto E.A. Adeboye saboda yin haka ya sabawa ka'idojin aikin jarida in ba haka zamu dauki mataki.
“Pastor E.A. Adeboye da cocin RCCG ba ta ba goyon bayan kowani dan takara kuma baza ta goyi kowani dan takara a zaben 2023 mai zuwa ba.”
Da na fadi warwas inda Buhari bai sanya hannu a dokar zabe ba – Adeleke
A wani labari - Jihar Osun - Zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya ce da ya sha kaye a zaben da aka yi ranar Asabar da ta gabata a hannun jam’iyyar, APC, inda shugaba Buhari bai rattaba hannu kan dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima ba. Rahoton VANGUARD
Ya ce:
“Na ji dadin nasarar da na samu, domin al’ummar Jihar Osun sun dade suna kwadayin ganin an dawo da kujerar da aka kwace mu su.
Asali: Legit.ng