Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya sa labule da gwamna Wike a Patakwal

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya sa labule da gwamna Wike a Patakwal

  • Tsohon gwamnan Zamfara kuma jigo a APC, Abdulaziz Yari, ya dira Patakwal, ya sa labule da gwamnan Ribas, Nyesom Wike
  • Rahoto ya nuna cewa Yari na isa gidan Wike da ke babban birnin jihar, babu wani ɓata lokaci suka shiga tattauna wa a sirrance
  • Jigan-jigan jam'iyyar APC sun jima suna zuwa Patakwal wurin Wike, ana tsammanin suna kokarin jawo ra'ayinsa ya bar PDP

Rivers - Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma babban jigon APC, Abdullaziz Yari, ya shiga ganawa da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a gidansa da ke Patakwal, babban birnin jihar ranar Talata.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Yari na dira gidan gwamna Wike da ke yankin Rumuepriokom, ƙaramar hukumar Obio/Akpor, ba tare da ɓata lokaci ba suka shiga ganawar sirri.

Yari ya ziyarci Wike a Patakwal.
Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya sa labule da gwamna Wike a Patakwal Hoto: @leadershipNGA
Asali: Twitter

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abun da manyan jiga-jigan siyasar biyu suka tattauna yayin ganawarsu amma ana tsammanin ba zai rasa nasaba a zaɓen 2023 ba, Daily Trust ta rahoto.

Yari da Wike
Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya sa labule da gwamna Wike a Patakwal Hoto: leadership
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnonin APC sun gana da Wike

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu gwamnoni uku na jam'iyyar APC sun ziyarci gwamna Wike a gidansa kwanakin baya.

Gwamnonin sun hada da Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Babajide Sanwo- Olu na jihar Legas da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Wike, jigo a jam’iyyar PDP, ana sa ran zai marawa dan takarar jam’iyyarsa, Atiku Abubakar baya, sai dai hasashe ya bayyana cewa gwamnan jihar Ribas bai ji dadi ba bayan an fasa ba shi tikitin mataimakin shugaban kasa.

A wani labarin kuma kun ji cewa Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo, Sanata mai ci ya fice daga jam'iyyar

Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa wato PDP ta yi rashin ɗaya daga cikin mambobinta a majalisar dattawan Najeriya.

Sanata Bassey Albert Akpan, ya fita jam'iyyar PDP domin cika burinsa na takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel