Guguwar sauya sheƙa: Ɗan majalisar dokokin jiha ya fice daga jam'iyyar APC

Guguwar sauya sheƙa: Ɗan majalisar dokokin jiha ya fice daga jam'iyyar APC

  • Ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa, Abdulaziz Ɗanladi, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar AA a hukumance
  • Kakakin majalisar dokokin Nasarawa, Ibrahim Abdullahi, yayin karanta wasikar Abdulaziz ya ce ya yi haka ne saboda rikicin cikin gida a APC
  • Jam'iyya mai mulkin Najeriya na fama da rikici tsakanin jiga-jiganta wanda hakan ya yi sanadin shan kaye a zaɓen Osun

Nasarawa - Mamba mai wakiltar mazaɓar Keffi ta gabas a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Abdulaziz Danladi, ya fice daga jam'iyyar APC a hukumance.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Ibrahim Abdullahi, shi ne ya bayyana haka yayin da yake karanta takardar murabus ɗin Abdulaziz daga kasancewa mamban APC a zaman majalisa ranar Litinin a Lafiya.

Majalisar dokokin Nasarawa.
Guguwar sauya sheƙa: Ɗan majalisar dokokin jiha ya fice daga jam'iyyar APC Hoto: dailynigerian
Asali: UGC

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto kakakin majalisar na cewa duba da abin da takardar ɗan majalisar ta ƙunsa, Mista Abdulaziz ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar Action Alliance, wato AA.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Wani mutumi na tsaka da murnar nasarar PDP a zaɓe Osun, ya harbe kansa da bindiga bisa kuskure

Meyasa ɗan majalisar ya ɗauki wannan matakin?

Yayin karanta takardar murabus ɗin ga mambobin majalisa, kakakin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan takarda ce daga Abdulaziz Ɗanladi, mamba mai wakiltar mazaɓar Keffi ta gabas, yana mai sanarwa gida cewa ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyyar APC."
"Abinda wasiƙar sa ta ƙunsa shi ne: Sanarwan sauya jam'iyya; ina mai sanar da gida cewa na fice daga jam'iyyar All Progressives Congress watau APC a hukumance."
"Na ɗauki wannan matakin ne duba da rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar wanda har yanzun ya gagari shugabanni su shawo ƙansa. Saboda haka na fita daga APC kuma na koma Action Alliance (AA)."

Tun bayan kammala zaɓen fidda gwani na APC a dukkan matakai, jam'iyyar ke fama da rikice-rikice wanda ya yi sanadin rasa jiga-jiganta zuwa wasu jam'iyyun adawa.

A wani labarin kuma Hadimin gwamna Tambuwal da dandazon mambobi sun sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo, Sanata mai ci ya fice daga jam'iyyar

Mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto shawara ta musamman ya ja masoyansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Honorabul Ibrahim Gidado, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar, ya samu kyakkyawar tarba daga jiga-jigan APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262