Mun san inda aka yi garkuwa da ’yan uwan tsohon gwamnan Bauchi – ‘Yan sanda

Mun san inda aka yi garkuwa da ’yan uwan tsohon gwamnan Bauchi – ‘Yan sanda

  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi ya bayyana cewa ‘yan sanda sun san inda ‘yan uwan tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Mu’azu suke
  • Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya kai ziyarar jaje ga iyalan Ahmed Muazu da al’ummar karamar hukumar Tafawa Balewa
  • CP Sanda Umar Mamman ya ce ‘yan fashin da suka yi garkuwa da iyalan Adamu Muazu suna neman naira miliyan 600 kafin su sake su

Jihar Bauchi - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi CP Umar Mamman Sanda ya bayyana cewa ‘yan sanda sun san inda ‘yan uwan tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Mu’azu suke, inda ya kara da cewa ‘yan fashin na neman naira miliyan 600 kafin su sake su. Rahoton Daily Trust

CP Sanda ya bayyana haka ne jiya a kauyen Boto lokacin da ya raka gwamna Bala Mohammed Abdulkadir domin jajantawa iyalan tsohon gwamnan da al’ummar karamar hukumar Tafawa Balewa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

Bauchi
Mun san inda aka yi garkuwa da ’yan uwan tsohon gwamnan Bauchi – ‘Yan sanda FOTO TVC
Asali: UGC

Ya ce:

“Mun san inda wadanda aka sace suke kuma muna yin iya kokarin mu don kubutar da su cikin koshin lafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Mohammed a nasa bangaren ya ce :

" yanzu ‘yan bindigar sun taba gwamnati tunda suka taba iyalan daya daga cikin tsohon gwamnonin mu. Zamu yi iya kokarin mu wajen ceto su.
"Wadannan ’yan iska sun ci mutuncin mu, kuma ba za mu kyallesu ba.

A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan tsohon Gwamnan Bauchi, inda suka kashe kanensa Mua’zu Danladi mai shekaru 25, sannan suka yi garkuwa da ‘yan uwansu uku, Hajiya Asma’u Alhaji Adamu, kanwar tsohon gwamnan, Malama Halima. Abdullahi, da Nura daya.

Kungiyar CAN ta yi korafi akan yawan sace-sacen Mambobinta a Najeriya

A wani labarin kuma, Kungiyar Kristocin Najeriya CAN, ta bayyana bakicin ciki da damuwa akan yadda sace Fastocin da mabiyan su ya zama ruwan dare a jihar Kaduna da wasu sassar Najeriya. Rahoton BBC

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari ya jawo muka rasa zaben Gwamna a Jihar Osun - Jagoran APC

Jagoran kungiyar CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya bayyana haka da yake tattaunawa da waikilan BBC, Inda ya ce :

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa