Zaɓen Gwamna: Oyetola, Ambode da sauran gwamnonin da suka sha ƙasa suna kan mulki

Zaɓen Gwamna: Oyetola, Ambode da sauran gwamnonin da suka sha ƙasa suna kan mulki

A wasu lokutan Gwamnonin da ke kan madafun iko kan rasa damar tazarce a Najeriya, a baya-bayan nan mutane sun shaida yadda karfin mulki ya gaza a zaɓen Osun da aka kammala.

Wasu gwamnoni a Najeriya sun sha kaye yayin da suka yi yunkurin ganin sun zarce zango na biyu a kan kujerun su a lokuta daban-daban, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Gwamnonin da suka gaza tazarce.
Zaɓen Gwamna: Oyetola, Ambode da sauran gwamnonin da suka sha ƙasa suna kan mulki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro muku waɗan nan gwamnonin da irin haka ta faru da su, ga su kamar haka:

1. Gwamna Oyetola na jihar Osun

Gwamnan jihar Osun da ke kan mulki yanzu haka, Gboyega Oyetola, na jam'iyyar APC ya sha ƙasa a hannun ɗan takarar babbar jam'iyyar hamayya PDP, Sanata Ademola Adeleke, a zaɓen gwamnan jihar da aka kammala ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Wani mutumi na tsaka da murnar nasarar PDP a zaɓe Osun, ya harbe kansa da bindiga bisa kuskure

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna ya samu kuri'u 375,027 yayin da abokin hamayyarsa, Adeleke, ya samu kuri'u 403,371, hakan ya ba shi damar lallasa gwamna mai ci.

Ambode na jihar Legas.
Zaɓen Gwamna: Oyetola, Ambode da sauran gwamnonin da suka sha ƙasa suna kan mulki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

2. Ambode a jihar Legas

Tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya rasa samun tazarce tun daga zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC.

A wani shirin kai tsaye, Ambode ya taya Babajide Sanwo-Olu murna bayan ya lallasa shi ya samu tikitin takara karkashin inuwar APC.

An bayyana Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri'u 970,851, ya kayar da Ambode mai kuri'u 70,901, hakan ya sa ya zama gwamna na farko da ya rasa tikitin jam'iyyarsa a 2019.

3. Mohammed Abubakar a jihar Bauchi

A jihar Bauchi makamancin hakan ta taɓa faruwa yayin da Sanata Bala Mohammed Abdulkadir, na PDP ya lashe zaɓen gwamna bayan lallasa gwamna mai ci a lokacin Mohammed Abdullahi Abubakar na APC.

Kara karanta wannan

Allah kadai ke zabar wanda zai mulki al’umma, Ministan Buhari ya yi martani bayan APC ta sha kaye a zaben Osun

Bayan fafatawa mai zafi a karshe Abubakar ya samu adadin kuri'u 500,625 yayin da tan takarar PDP, Abdulƙadir, ya samu jumullan ƙuri'u 515,113.

Abubakar ya zama gwamnan jihar Bauchi ne a zaɓen 2015 kuma ya gaza kai bantensa yayin da ya yi kokarin tazarce a 2019.

4. Bindow a jihar Adamawa

Jibrila Bindow, ɗan takarar gwamna na APC a jihar Adamawa kuma gwamna mai ci a lokacin ya sha kaye a zaɓen 2019.

Bindow ya samu kuri'u 336,386 yayin da abokin hamayyarsa na PDP, Ahmadu Fintiri, ya samu kuri'u 376,552, inda ya ba shi ratar kuri'u sama da 40,000.

A watan Maris, INEC ta ayyana zaɓen jihar Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba saboda adadin ƙuri'un da aka soke ya zarce yawan ratar da ke tsakanin Bindow da Fintiri.

Bayan sake zaɓe a akwatunan da abun ya shafa, hukumar INEC ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

5. Fayemi a jihar Ekiti

Kayode Fayemi.
Zaɓen Gwamna: Oyetola, Ambode da sauran gwamnonin da suka sha ƙasa suna kan mulki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan doguwar fafatawa da tafka muhawara a Kotu da ɗan takarar jam'iyyar Action Congress da aka rushe a Najeriya, Dakta Kayode Fayemi, wanda daga baya aka tabbatar da shi a halastaccen gwamna, ya shiga Ofis a 2010.

Sai dai yunkurin gwamnan na zarce wa kan kujerarsa bai yi nasara ba, ɗan takarar PDP, Ayodele Fayose, ya lallasa shi a zaɓe.

A wani labarin kuma Hadimin gwamnan PDP a arewa da dandazon mambobi sun sauya sheƙa zuwa APC

Mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto shawara ta musamman ya ja masoyansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Honorabul Ibrahim Gidado, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar, ya samu kyakkyawar tarba daga jiga-jigan APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262