Gwamna Fayemi ya sallami baki ɗaya hadimansa daga bakin aiki
- Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Kayode Fayemi, ya amince da ƙare aikin manyan hadimansa na siyasa daga 31 ga Yuli
- Yayin da wa'adin mulkinsa ke gab da ƙarewa, gwamnan ya yi haka ne domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin sauki
- A watan da ya gabata ne al'ummar jihar Ekiti suka zabi sabon gwamnan da zai jagorance su na tsawon shekara huɗu
Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sallami dukkan hadimansa na siyasa da ya naɗa a gwamnatinsa yayin da lokacin miƙa mulki ke kusantowa.
A cewar wata sanarwa da Daily Trust ta tattaro, gwamnan ya ɗauki matakin ne domin biyayya ga dokokin miƙa mulki na jiha da kuma tabbatar da an biya kowane mai rike da Ofis haƙƙinsa da alawus ɗin zango.
Sanarwar na ɗauke na sa hannun Sakataren gwamnatin jihar, Foluso Daramola, kuma an raba wa manema labarai kwafinta a Ado-Ekiti, babban birnin jihar a ƙarshen makon nan.
Sakataren ya ce gwamna Fayemi ya kawo karshen aikin masu hidimta masa kuma matakin zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da bayyana cewa hakan zai ba gwamnati damar biyan mutanen da lamarin ya shafa hakkokin su da sauran alawus ɗin su da aka riƙe, domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi.
Wani sashin sanarwan ya ce:
"An kafa kwamitin miƙa mulki da sauran kwamitoci da zasu yi aiki wajen miƙa mulki daga gwamnati mai ci zuwa sabuwar gwamnati da al'umma suka zaɓa cikin sauki."
"Ɗaya daga cikin nauyin da ya rataya kan kwamitin kamar yadda dokokin miƙa mulki na jihar Ekiti suka tanada, shi ne tabbatar da biyan masu rike da ofisoshin siyasa haƙƙinsu haɗi da alawus ɗin zangon mulki."
Hadiman da sallamar ta shafa
Bayan haka, a ruwayar Punch, Sakataren ya ambaci ofisoshin da sallamar ta shafa da cewa:
"Mai girma Dakta John Kayode Fayemi, ya amince da kawo ƙarshen aikin manyan mataimakansa na musamman, mataimaka na musamman, hadiman sashin fasaha daga ranar 31 ga watan Yuli, 2022."
A wani labarin kuma kun ji cewa Wani mutumi na tsaka da murnar nasarar PDP a zaɓe Osun, ya harbe kansa da bindiga bisa kuskure
Wani mutumi mai suna, Sunday Akingbala ya harbi kansa da kansa yayin da yake murnar nasarar da ɗan takarar PDP ya samu a zaɓen gwamnan jihar Osu.
A rahoton jaridar The Cable, mutumin wanda mamba ne kuma magoyin bayan jam'iyyar PDP ya nuna tsantsar farin ciki da nasarar Sanata Ademola Adeleke a zaɓen da ya gudana ranar Asabar.
Asali: Legit.ng