'Ɗan PDP ya bindige kansa yayin murnar nasarar jam'iyyarsa a zaɓen Osun
- Yayin da yake nuna jin daɗinsa da nasarar PDP, wani mutumi ya harbi kansa da bindiga a Ile-Ife ranar Lahadi
- Bayanai sun nuna cewa an garzaya da shi wani Asibiti mafi kusa kafin daga bisani a maida shi Asibitin koyarwa
- Sanata Adeleke na jam'iyyar PDP ya samu nasarar zama zaɓaɓɓen gwamna bayan kammala zaɓe ranar Asabar a jihar Osun
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Osun - Wani mutumi mai suna, Sunday Akingbala ya harbi kansa da kansa yayin da yake murnar nasarar da ɗan takarar PDP ya samu a zaɓen gwamnan jihar Osu.
A rahoton jaridar The Cable, mutumin wanda mamba ne kuma magoyin bayan jam'iyyar PDP ya nuna tsantsar farin ciki da nasarar Sanata Ademola Adeleke a zaɓen da ya gudana ranar Asabar.
Rahoto ya nuna cewa yayin murna, Sunday, wanda mamba ne a hukumar tsaron Amotekun, ya harbi kansa a Ile Ife ranar Lahadi.
Allah kadai ke zabar wanda zai mulki al’umma, Ministan Buhari ya yi martani bayan APC ta sha kaye a zaben Osun
Tuni dai mutane suka yi gaggawar kai shi Asbitin Seventh Day Adventist Church da ke Lagere a Ile-Ife amma daga baya an maida shi Asibitin koyarwa na jami'ar Obafemi Awolowo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda PDP ta lashe zaɓen gwamna a Osun
Sanata Adeleke, sabon gwamna mai jiran gado a jihar Osun, ya samu kuri'u 403,371, da haka ya lallasa babban abokin takararsa Gboyega Oyetola, gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam'iyyar APC.
A zaɓen wanda INEC ta gudanar ranar Asabar 16 ga watan Yuli, 2022, gwamnan Osun Oyetola na APC ya samu kuri'u 375,027, Vanguard ta tabbatar a wani rahoto.
Ɗan takarar babbar jam'iyyar hamayya watau PDP ya lashe kananan hukumomi 17 daga cikin 30 dake faɗin jihar yayin da gwamnan ya lashe guda 13.
Baki ɗaya yan takaran biyu da ke sahun gaba sun fafata da juna a babban zaɓen gwamnan jihar wanda ya gabata a shekarar 2018.
Ko a wancan Lokacin, Sanata Adeleke ne ke kan gaba da sakamakon da ya fara fitowa kafin daga baya hukumar zaɓe ta ƙasa ta ayyana zaɓen a matsayin, "wanda bai kammalu ba."
INEC ta ayyana Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan sake gudanar da zaɓe a wasu akwatunan zaɓe a jihar wancan lokaci.
A wani labarin kuma Atiku Ya Taya Adeleke Murnar Lashen Zaben Gwamnan Jihar Osun
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya Ademola Adeleke murnar lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Alhaji Atiku Abubakar ya ce nasarar Ademola Adeleke a zaben jihar Osun ya nuna mulki a hannun al'umma yake.
Asali: Legit.ng