Zaben Osun: Dan takarar PDP ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta na nan tana harhada sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka yi a ranar Asabar
- Zuwa yanzu, dan takarar jam'iyyar PDP mai adawa, Sanata Ademola Adeleke ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30
- Shi kuma gwamna mai ci kuma dan takarar jam'iyyar APC kuma gwamna mai ci, Adegboyega Oyetola, yana da kananan hukumomi 13
Osun - Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30, Channels Tv ta rahoto.
Gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adegboyega Oyetola, ya kawo sauran kananan hukumomi 13 da suka yi saura.
Hakan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta tattara sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli.
Shirin tattara sakamakon, wanda ya fara a safiyar Lahadi, 17 ga watan Yuli, yana nan yana gudana a ofishin hukumar INEC da ke Osogbo, babbar birnin jihar ta Osun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daily Trust ta rahoto cewa jami’an zabe na nan suna shirin kammala yin gyare-gyaren da ya kamata a takardun zaben.
Zaben Osun: APC ta ji kunya, Gwamna ya rasa akwatin gidan Gwamnati a hannun PDP
A baya mun ji cewa mai girma gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola bai iya samun nasara a akwatin da aka kada a gidan gwamnati da ke Osogbo ba.
Rahoton da This Day ta fitar a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli 2022, ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta lashe akwatin rumfar gidan gwamnati.
A halin yanzu ana zaben gwamna a jihar Osun, inda Adegboyega Oyetola yake neman tazarce.
Asali: Legit.ng