Labari mai zafi: An kwantar da Osinbajo a asibiti, Likitoci na shirin yi masa aiki
- Farfesa Yemi Osinbajo ya na gadon asibiti a halin yanzu, za ayi masa aiki a kafansa
- A shafin Twitter, Mataimakin shugaban kasar ya bada sanarwar an kwantar da shi
- Yemi Osinbajo yana zargin wajen buga wasan ‘Squash’ ne ya samu larura a kafarsa
Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yana kwance a asibiti, ana sa ran cewa za ayi masa aiki.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Yemi Osinbajo ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli 2022.
A gajeren jawabin da ya fitar da karfe 7:00 na yammacin yau, Farfesa Yemi Osinbajo bai iya bayyana asibitin da yake kwance ba.
Amma an fahimci Mataimakin shugaban kasar yana asibiti yanzu, kuma yana fama da matsalar ciwon kafa ne da ya addabe shi.
“An kwantar da ni a asibiti yau domin ayi mani aiki saboda yawan ciwon kafa da nake fama da shi.”
“Watakila na samu larurar ne a wajen buga wasan Squash.” – Yemi Osinbajo
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A rahoton da The Cable ta fitar dazu, ta bayyana cewa Laolu Akande ya tabbatar da cewa Mai gidan na sa yana jinya, za ayi masa aiki.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar ya fitar da jawabi irin na mai gidansa, ya ce ciwon kafa yake fama da ita tun tuni.
Ba kasafai aka saba jin Osinbajo mai shekara 65 da haihuwa bai da lafiya ba.
Masana sun ce masu buga wasan Squash kan gamu da matsalolin ciwon kafa, hannuwa ko kuma baya, amma bai cika yin kamari ba.
Sai dai irin wadannan larurori su kan jawo mutum ya samu rauni wurin tafiya da ayyukansa, don haka Likitoci kan iya yin karamin aiki.
Mai buga wasa zai iya zamewa a fili ko kuma kwallo ta buge shi musamman a ido.
Asali: Legit.ng