Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar PDP ta lashe rumfar zabe ta farko a zaɓen Osun

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar PDP ta lashe rumfar zabe ta farko a zaɓen Osun

Osun - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga gaba da sakamakon da ya fara fita wanda ma'aikatan hukumar zaɓe ta ƙasa INEC suka bayyana a jihar Osun ranar Asabar.

A rumfar zaɓe ta 05, gunduma ta 007, ƙaramar hukar Ilesa ta yamma, Sanata Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya tashi da kuri'u 49, yayin da gwamna mai-ci, Gboyega Oyetola, na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 17.

Daily Trust ta rahoto cewa adadin masu kaɗa kuri'a 120 ne suka yi rijistar zaɓe a ruɓfar zaɓen kuma ma'aikatan INEC sun tantance mutum 71 a ranar zaɓe watau yau Asabar.

Ku saurari ƙarin bayani...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262