2023: Jam'iyyar PDP ta gamu da cikas, Ɗan takarar gwamna kuma Sanata Mai Ci ya fice

2023: Jam'iyyar PDP ta gamu da cikas, Ɗan takarar gwamna kuma Sanata Mai Ci ya fice

  • Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa wato PDP ta yi rashin ɗaya daga cikin mambobinta a majalisar dattawan Najeriya
  • Sanata Bassey Albert Akpan, ya fita jam'iyyar PDP domin cika burinsa na takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a zaɓen 2023
  • Albert Akpan ya ja daga da ɗan takarar gwamna da gwamna mai ci ke goyon bayan, inda ya kalubalanci lamarin a Kotu

Akwa Ibom - Ɗan takarar tikitin gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom, Bassey Albert, ya fice daga jam'iyyar, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mista Albert, wanda yanzu haka shi ne Sanata mai wakiltar mazaɓar Akwa Ibom ta arewa maso gabas a majalisar Dattawa, ya bayyana haka ne a wata takarda da ya aike wa shugaban PDP.

Sanatan ya aike da takardar ga shugaban PDP na gundumarsa a yankin ƙaramar hukumar Ibiono Ibom ɗauke da kwanan watan 15 ga watan Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya ana dab da zaɓe, wata jam'iyyar adawa ta koma bayan ɗan takararta

Sanata Bassey Albert Akpan
2023: Jam'iyyar PDP ta gamu da cikas, Ɗan takarar gwamna kuma Sanata Mai Ci ya fice Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Albert ya bayyana cewa ya yanke shawarin yin murabus daga kasancewa mamban PDP ne domin samun damar shiga takarar gwamna a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani sashin takardar Murabus din wacce Vanguard ta haɗa a rahotonta ya ce:

"Kamar yadda kowa ya sani burina na zama gwamna ba na ƙashin kaina bane, gamayyar muradan mutanen mu ne duba da ƙa'idoji, adalci da daidaito domin cimma gaci a Akwa Ibom."
"Bayan faɗaɗa shawari da Allah, iyalai, abokai, magoya baya da masu fatan Alkairi a Akwa Ibom da sassan duniya; ya fito ƙarara cewa Allah-Allah da burin mu ba zasu cimma gaci ba ƙarkashin inuwar PDP."
"Saboda haka, damuwa da rashin jin daɗin mutane suka sa muka ga bukatar ɗaukar matakin cika burin, haka ya tilasta mun murabus daga kasancewa ta mamba a jam'iyyar PDP."

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana uku a rufe, jam'iyyun su Kwankwaso da Sawore ba su kai sunayen yan takararsu na jihohi ba, INEC

Wace jam'iyya zai koma?

Duk da cewa Sanatan bai fayyace jam'iyyar siyasan da zai nufa don cika wannan burin na shi ba, amma jita-jita ta karaɗe ko ina cewa zai koma jam'iyyar Young Progressive Party (YPP).

Takardar murabus ɗin Albert ta karaɗe shafin sada zumunta Whatsapp jim kaɗan bayan sanatan ya yi rashin nasara a ƙarar da shigar gaban babbar Kotun tarayya da ke zama a Abuja.

A ƙarar, Sanata Albert ya ƙalubalanci matakan da jam'iyyar PDP ta bi wajen zaƙulo Deleget na wucin gadi da suka kaɗa kuri'u a zaɓen fidda gwani.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya ana dab da zaɓe, wata jam'iyyar adawa ta koma bayan ɗan takararta

Awanni kafin fara kaɗa kuri'a, jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya a jihar Osun.

Jam'iyyar AD wato Alliance for Democracy ta umarci baki ɗaya masoya da magoya baya su dangwalawa gwamna Oyetola a zaɓen gobe.

Kara karanta wannan

Kokarin shawo kan rikicin PDP ya gamu da cikas, Wani Jigo a shiyyar arewa ya fice daga jam'iyyar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262