Osun 2022: Jam'iyyar adawa ta ayyana goyon bayan ɗan takarar jam'iyyar APC

Osun 2022: Jam'iyyar adawa ta ayyana goyon bayan ɗan takarar jam'iyyar APC

  • Awanni kafin fara kaɗa kuri'a, jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya a jihar Osun
  • Jam'iyyar AD wato Alliance for Democracy ta umarci baki ɗaya masoya da magoya baya su dangwalawa gwamna Oyetola a zaɓen gobe
  • Jam'iyyar wacce tana ɗaya daga cikin waɗan da INEC ta soke rijistar su, ta taya Bola Ahmed Tinubu murna

Osun - Jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) ranar Jummu'a ta ayyana cikakken goyon bayanta ga tazarcen gwamna Gboyega Oyetola, ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Osun.

Premium Times ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban kwamitin tsare-tsare na AD, Abdallah Muktar, da Sakatare Kola Ajayi, suka sa wa hannu.

Sanarwan ta roki mambobin jam'iyyar da su zaɓi gwamna Oyetola ya zarce kan kujerarsa kamar yadda zasu zaɓi jam'iyyar AD.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle zuwa APC

Yaƙin neman zaɓe.
Osun 2022: Jam'iyyar adawa ta ayyana goyon bayan ɗan takarar jam'iyyar APC Hoto: Kebbi State Government/facebook
Asali: Facebook

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa jam'iyyar AD na ɗaya daga cikin jam'iyyun siyasa a Najeriya da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta soke rijistar su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon haka jam'iyyar ba ta da ikon tsayar da ɗan takara a zaɓen gwamnan da za'a yi gobe. Sanarwan da AD ta fitar ta ce:

"Baki ɗaya mambobin mu, masu goyon baya da masu ruwa da tsaki, daga wannan sanarwa muna umartan su fita kuma su dangwalawa gwamna Oyetola saboda ya cancanci a sake ba shi dama."
"Ba tare da nuna banbanci ba muna kira da al'ummar jihar Osun su zaɓi gwamna Oyetola domin ya cigaba da jagorancin da ya ɗakko."

Jam'iyyar AD ta taya Bola Tinubu murna

Hak zalik jam'iyyar ta kuma ta ya Bola Ahmed Tinubu murna bisa lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a babbam zaɓen 2023 dake tafe.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana uku a rufe, jam'iyyun su Kwankwaso da Sawore ba su kai sunayen yan takararsu na jihohi ba, INEC

Sanarwan ta kara da tuna baya, inda ta bayyana cewa Tinubu na ɗaya daga cikin gwamnonin da jam'iyyar ta kai kan mulki a zaɓen 1999, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kokarin shawo kan rikicin PDP ya gamu da cikas, Wani Jigo a shiyyar arewa ya fice daga jam'iyyar

Babban jigon PDP kuma ma'aji a reshen shiyyar arewa maso gabas, Abba Itas, ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya.

Honorabul Abba ya bayyana cewa ya yi haka ne sakamakon rashin adalci da zaluntar da aka yi wa gwamna Wike na Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262