Zamfara: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle
- Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a birnin Shehu ta ce babu ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya
- Da take yanke hukunci, ta tabbatar da hukuncin farko da babbar Kotun tarayya ta Gusau ta yanke kan gwamna Bello Matawalle
- A watan Fabrairu, Kotun tarayya ta yi watsi da karar tsige gwamnan kan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - Kotun ɗaukaka ƙara da ke Sakkwato ta yi fatali da ƙarar da ta nemi a tsige gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara kan sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Yayin yanke hukunci ranar Laraba, Kotun ta tabbatar da hukuncin da babbar Kotun tarayya dake Gusau ta yanke, wanda ya yi watsi da ƙara kan matakin gwamnan.
Lauyan Matawalle, Mike Ozekhome (SAN), shi ne ya tura cikakken bayanin hukuncin da Kotun ta yanke ga jaridar Premium Times ranar Jumu'a.
Kwamitin Alƙalai uku na Kotun ɗaukaka kara karkashin jagorancin mai shari'a, A. A. Gumel, sun yanke hukunci ba tare da tantama ba cewa ba ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa kan ya sauya sheka daga jam'iyya zuwa wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bisa hujjar abin da ke ƙunshe a sashi na 40 a kundin mulkin Najeriya, Kotun ta yanke cewa gwamna na da damar sauya sheka daga jam'iyya zuwa wata ba tare da rasa kujerarsa ba.
Bugu da ƙari, Kotu ta ƙara da cewa da zaran gwamnan ya shiga Ofis bayan karɓan rantsuwar kama aiki, ya ta shi daga ƙarƙashin kulawar jam'iyyar da ta ɗauki nauyinsa.
A cewar Kotun za'a iya tsige gwamna daga kujerarsa ne kaɗai idan ya yi karan tsaye ga abinda sashi na 180, 188 da 189 na kundin tsarin mulki 1999 ya ƙunsa.
A sanarwar da lauyan ya aike wa jaridar ya ce:
"An warware komai yadda tsagin gwamna ke so, an yi da watsi da ƙarar da suka ɗaukaka kuma an tabbatar da hukunci da babbar Kotun tarayya ta yanke ranar 7 ga Fabrairu, 2022."
An ƙara cin tarar masu ƙara
Bayan tarar miliyan ɗaya da Kotun baya ta umarci a biya waɗan da aka shigar ƙara, Kotun ɗaukaka ƙaran ta ƙara maka tarar wata Miliyan ɗaya daban da masu ƙara zasu bai wa gwamna da mataimakinsa.
Mahdi Gusau ya yi rashin nasara a Kotu
Haka nan kuma Kotun ta yi fatali da bukatar tsakiyar ƙara da Mahdi Gusau ya shigar, tsohon mataimakin gwamna da majalisa ta tsige, wanda ya nemi a ayyana shi gwamna sakamakon Matawalle ya bar PDP.
Ta yanke cewa Mahdi Aliyu ba zai karbi ragamar mulki daga hannun Matawalle ba saboda kawai gwamnan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
A wani labarin na daban kuma kun ji cewa PDP ta shigar da INEC kara dan neman hana Tinubu da Obi tsayawa takara
Jam’iyyar PDP ta bukaci INEC da ta haramtawa jam’iyyar Labour da jam'iyyar APC shiga zaben 2023.
Jam’iyyar ta bukaci kotun da ta haramtawa ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun biyu takara saboda sun sauya sunayen abokan takararsu.
Asali: Legit.ng