Idan aka kara kai wani hari, Za Mu Sayi Bindiga mu ba Mutanen mu – Akeredolu
- Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa zai baiwa al’ummar jihar Ondo makamai domin kare kansu idan ‘yan ta’adda suka sake kai wa jihar sa hari
- Akeredolu ya bai wa jam'ian Yansanda da jami'an Amotekun kyautar motoci 50 dan inganta tsaro a jihar Ondo
- Gwamna Rotimi Akeredolu yace kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar sa shine abu mafi fifiko a gareshi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa zai baiwa al’ummar jihar Ondo makamai domin kare kansu idan ‘yan ta’adda suka sake kai hari a jihar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da yake gabatar da motoci 50 da suka dace da jami’an tsaro a jihar, ciki har da kungiyar tsaro ta jihar Ondo, wacce aka fi sani da Amotekun.
Da yake tunawa da kisan da aka yi wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Church, Owo, a ranar 5 ga watan Yuni, 2022, gwamnan ya koka da yadda ‘yan sanda ba su iya yin komai ba a lokacin da aka kai musu rahoton faruwar lamarin saboda ba su da motar da za ta iya aiki.

Asali: UGC
Ya ce daga baya Jami’an Amotekun ne suka fatattaki ‘yan ta’addan, amma lokaci ya kure.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Akeredolu ya ce:
“Kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar sa shine abu mafi fifiko a gareshi.
“Idan aka kara kai wa mutanen mu hari a nan, za mu umarce da su sami bindigogi don kare kansu. Kuma muma zamu sayan musu bindigogi domin su kare kansu.
2023: Jerin sunayen yan takarar mataimakin shugaban kasa 10 da kwamitin APC ya gabatarwa Tinubu
A wani labari kuma, Kafin bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC mai mulki, an kafa wani kwamiti don ba wanda ke rike da tutar jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu shawara kan wanda zai tsayar a matsayin abokin takara.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli, kwamitin ya gabatarwa Tinubu da sunayen yan takara 10.
Asali: Legit.ng