Kwamishina ta yi murabus daga kujerarta awanni bayan gwamna ya canza mata ma'aikata

Kwamishina ta yi murabus daga kujerarta awanni bayan gwamna ya canza mata ma'aikata

  • Wata kwamishina a gwamnatin jihar Ondo ta rubuta takardar aje aiki awanni kaɗan bayan gwamna ya canza mata ma'aikata
  • Gwamna Akeredolu, yayin bai wa sabbin kwamishinoni biyu da ya naɗa shahadar kama aiki, ya ɗan yi garambawul a majalisar
  • Misis Adeyanju ta ce ta ɗauki matakin murabus ne bisa ra'ayin kanta domin sauke wasu nauye-nauye baya ga siyasa

Ondo - Wata kwamishina a jihar Ondo, Yetunde Adeyanju, ta miƙa takardar barin aiki awanni kalilan bayan gwamna Rotimi Akeredolu, ya canza mata wurin aiki.

Vanguard ta ruwaito cewa Adeyanju, wacce a baya take rike da ma'aikatar ruwa da duba tsaftar mahalli, ta samu canjin wurin aiki ne zuwa ma'aikatar tsare-tsare da raya karkara.

Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.
Kwamishina ta yi murabus daga kujerarta awanni bayan gwamna ya canza mata ma'aikata Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Gwamnan ya canza wa kwamishinan wurin aiki ne yayin da ya gudanar da wani ƙaramin garambawul a majalisar kwamishinoninsa ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Babu wata yarjejeniya tsakanimu da ASUU, inji gwamnatin Buhari

Gwamna Akeredolu ya bai wa sabbin kwamishinoni biyu, Sowore Samson da Ologbese Joseph, rantsuwar kama aiki, bisa haka ya yi garambawul da ya shafi ita Adeyanju da Misis Olateju wacce ke rike da ma'aikatar haɗin kan yanki da waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garambawul din ya maida Misis Olateji ma'aikatar yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, yayin da tsohon kwamishinan ma'aikatar tsare-tsare da raya karkara ya koma ma'aikatar ruwa da duba mahalli.

Meyasa ta yi murabus?

Sai dai Misis Adeyanju, a takardar murabus ɗinta, ta yi godiya ga gwamna Akeredolu bisa damar da ya bata na yi wa al'ummar jihar Ondo aiki.

Ta kafa hujjar dalilin aje aikinta da, "Haka nan bisa ra'ayin kanta domin ta samu cikakken lokacin sauke wasu nauye-nauyen da ke kanta baya ga siyasa."

Amma wata majiya ta ce kwamishinan, "Bata ji daɗin sabuwar ma'aikatar da gwamnan ya maida ita ba," shiyasa ta yi murabus.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Wa Babachir Lawal Martani: Gidauniya Ta Bata Taba Tilastawa Kirista Karbar Musulunci Ba

A wani labarin kuma Gwamnan Imo ya bugi kirjin cewa kowane ɗaya daga cikin gwamnonin APC 22 zai tabbatar ya kawo jiharsa a zaɓen 2023

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi ikirarin cewa kowane gwamna daga cikin gwamnonin cigaba na APC zai tabbatar jam'iyya ta yi nasara a jiharsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Uzodimma ya yi wannan furucin ne a Daura, jihar Katsina lokacin da suka je ziyarar barka da Sallah ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262