Bayan gaza samun tikitin Shugaban kasa, Jigon APC ya gagara samun tikitin Sanata

Bayan gaza samun tikitin Shugaban kasa, Jigon APC ya gagara samun tikitin Sanata

  • Godswill Akpabio yana shari’a da Udom Ekpoudom a game da takarar Sanata a jihar Akwa Ibom
  • Tsohon Ministan harkokin Neja-Delta ya dawo, yana so APC ta ba shi tikitin Sanata a zaben 2023
  • Udom Ekpoudom yana ikirarin shi ne wanda ya lashe zaben fitar da gwani da aka shirya a Mayu

Akwa Ibom - Tsohon Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio ya gamu da tasgaro a yunkurin sa na zama ‘dan takaran Sanata a jihar Akwa Ibom.

Premium Times ta kawo rahoto Godswill Akpabio bai yi nasara wajen karbe takara daga hannun tsohon mataimakin shugaban ‘yan sanda, Udom Ekpoudom.

Masu neman takaran Sanatan su na shari’a ne a babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja.

Mai shari’a D Okorowo ya saurari karar da Lauyan Mosta Udom Ekpoudom ya shigar, yana mai neman a ayyana ‘dan siyasar a matsayin ‘Dan takaran APC.

Kara karanta wannan

FG ta fitar da jerin sunayen wasu daraktoci 14 don zabar Akanta Janar a cikinsu

Lauyan da ya kai kara kotu ya bukaci hukumar INEC ta tabbatar da Ekpoudom a matsayin ‘dan takaran Sanatan yankin Akwa Ibom na Arewa maso yamma.

Alkali D Okorowo ya umarci hukumar INEC ta gabatar da takardun zaben fitar da gwanin da jam’iyyar APC ta shirya a ranar 27 ga watan Mayun 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Minista
Buhari da tsofaffin Ministocinsa Hoto: www.idomavoice.com
Asali: UGC

Sahara Reporters ta ce kotu ta bada umarni kawo takarda ko wasika daga APC da ke nuna an canza ‘dan takarar Sanata a Akwa Ibom ta Arewa ta yamma.

Victor Odjemu shi ne lauyan da ya tsayawa mai neman zama Sanatan na APC a zabe mai zuwa, yayin da shi kuma Umeh Kalu ya wakilci Sanata Akpabio.

A wajen hukumar zabe ta kasa watau INEC, Ekpoudom ne ainihin ‘dan takaran APC ba tsohon Ministan wanda ya taba wakiltar jihar a majalisar dattawa ba.

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

Duk da haka, APC ta ki bada sunansa, ta hakikance a kan cewa Akpabio ne wanda aka ba tuta.

Akpabio ya nemi tikitin shugaban kasa ne, daga baya ya janyewa Bola Tinubu. Bayan haka sai ya dawo jiharsa domin a ba shi takarar ‘dan majalisa a zaben badi.

Rigimar APC a Ribas

A jihar Ribas, an ji labari APC ta gamu da cikas domin rigimar Sanata Magnus Abe da tsohon Ministan Tarayya, Rotimi Amaechi ba ta zo karshe ba har yau.

Sanata Abe ya ce ba zai goyi bayan wanda jam’iyyar APC ta ba takara ba domin yana ganin babu gudumuwar da Tony Cole ya taba ba APC a tarihin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng