Tsohon ɗan majalisar tarayya da wani babban jigon APC sun yi murabus daga jam'iyyar
- Tsohon ɗan majalisar tarayya daga jihar Ribas, Elder Chidi Wihioka, ya sanar da ficewa daga jam'iyyar APC
- Awanni 24 kafin haka, tsohon muƙaddashin NDDC, Dame Ibim Semenitari, ya tattara kayansa ya bar APC mai mulkin Najeriya
- Wihioka ya ce duk da ya bar APC zai cigaba da goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Rivers - Wani babban jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon mamba a majalisar dokokin tarayya, Elder Chidi Wihioka, ya yi murabus daga jam'iyyar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne awanni 24 bayan wani tsohon muƙaddashin daraktan hukumar raya Neja Delta, Dame Ibim Semenitari, ya fice daga jam'iyyar APC.
Lokacin da ya rike kujarar ɗan majalisa, Wihioka, ya wakilci mazaɓar Ikwerre/Emuoha daga jihar Ribas majalisar dokoki ta tarayya.
Kokarin ɗinke ɓarakar APC ya gamu da babban cikas, Jigo kuma shugaban kwamitin sulhu ya fice daga jam'iyyar
Ya sanar da matakin murabus dinsa a wata wasika da ya aike wa shugaban APC na gundumar da ya fito Elele ta uku a jihar Ribas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wasiƙar, Honorabul Wihioka, ya bayyana cewa ya kai ga matakin ficewa daga jam'iyyar ne saboda yadda akalarta ta koma hannun mutum ɗaya, a cewarsa APC ta koma aljihunsa.
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Ina son sanar da kai a hukumance cewa na yi murabus daga jam'iyyar All Progressive Congress, APC. Na ɗauki wannan matakin ne saboda yadda komai ya koma hannun mutum ɗaya kuma ina ganin shi ya mallaki APC a Ribas."
"Kuma mutumin ya hana zaman lafiya ya samu wurin zama a cikin jam'iyya ta hanyar ba kowane mamba damar taka rawar da ya dace. Zan sanar da jam'iyyar da na koma idan na gano wacce ta dace da ni."
Duk da na fita zan cigaba da goyon bayan Tinubu - Wihioka
Sai dai ɗan majalisar ya ƙara da cewa duk jam'iyyar da ya tsinci kansa zai cigaba da goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
"Matakin da na ɗauka ba zai shafi goyon bayan da nake wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ba domin duk inda na tsinci kaina ba zan daina goyon bayansa ba."
A wani labarin kuma Gwamana ya karɓi jiga-jigan APC da mambobi 20,000 na jam'iyyu da suka sauya sheka zuwa PDP
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya karbi masu sauya sheƙa 20,000 daga jam'iyyu zuwa jam'iyyarsa PDP.
Da yake jawabi a wurin taron, gwamnan ya ce sauya shekar dubbanin mutanen alama ce da ke nuna Akwa Ibom jihar PDP ce.
Asali: Legit.ng