Gwamna ya karɓi masu sauya sheƙa sama da 20,000 zuwa jam'iyyar PDP a jiharsa
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya karbi masu sauya sheƙa 20,000 daga jam'iyyu zuwa jam'iyyarsa PDP
- Da yake jawabi a wurin taron, gwamnan ya ce sauya shekar dubbanin mutanen alama ce da ke nuna Akwa Ibom jihar PDP ce
- Ya roki Mambobi da masu ruwa da tsaki su rungumi masu sauya shekan kuma su haɗa kai da su don ci da jam'iyya gaba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya karɓi dubbannin mambobin jam'iyyar PDP, waɗan da suka fice a baya, yanzu kuma suka sake dawowa inuwar laima.
Da yake jawabi a ƙarshen makon nan a wurin taron jam'iyyar PDP na gundumar Awa Iman 1 wanda ya gudana a ƙaramar hukumar Onna, gwamnan ya bayyana cigaban a matsayin wata babbar alamar mamayar da PDP ta yi a siyasar jihar.
Gwamna Emmanuel ya tabbatar wa yan siyasan da suka dawo gida cewa za'a ɗauke su tamkar yan gida ba tare da nuna wani banbanci ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma roƙi mambobin jam'iyyar PDP a faɗin sassan gundumomi 329 da ke jihar Akwa Ibom da su rungumi masu sauya sheƙar sannan su haɗa kai don cigaban jam'iyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabinsa gwamnan ya ce:
"Muna gudanar da taron gunduma ne domin sake duba tsarukan da muka kafa a gundumomi, mu yi nazari kuma mu karɓi masu sauya sheƙa zuwa jam'iyyar mu."
"A baki ɗaya gundumomi 329 da muke da su a jihar nan mun karɓi mutane 20,000 da suka dawo cikin inuwar jam'iyyar mu, kuma ba bu ta yadda za'ayi mu shirya tarbar waɗan nan mutanen a wuri ɗaya."
"Abin da muke yi yau na ƙara tabbatar wa al'umma cewa nan jihar PDP ce kuma a shirye muke mu fita filin daga kuma mu lashe wasan."
Kokarin ɗinke ɓarakar APC ya gamu da babban cikas, Jigo kuma shugaban kwamitin sulhu ya fice daga jam'iyyar
Meyasa tun farko suka bar PDP?
A ruwayar Punch, ɗaya daga cikin masu sauya shekan, tsohon mataimakin Ciyaman na ƙaramar hukumar Onna, Julius Okon, ya ce ya bar PDP ne a baya saboda alƙawarin da wasu makusanta suka masa a wasu jam'iyyu.
Ya ce ya zaɓi ya sake dawowa daga jam'iyyar APC zuwa PDP saboda a nan ne ake ganin kimarsa.
A wani labarin kuma Kokarin ɗinke ɓarakar APC ya gamu da babban cikas, Jigo kuma shugaban kwamitin sulhu ya fice daga jam'iyyar
Shugaban kwamitin sulhu da zaman lafiya na jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya.
Dakta Dawari George, ɗan amutun tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sanar da haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban APC.
Asali: Legit.ng