Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida daga Faransa ranar Sallah

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida daga Faransa ranar Sallah

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu ya baro Faransa ya dawo Najeriya
  • Ahmed Tinubu yayi ganawar siiri da shugabankasa Muhammadu Buhari kafin ya tafi kasar Faransa a makon da ya gabata
  • Ana sa ran Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu zai bayyana abokin takarar sa bayan ya dawo daga tafiya

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo Najeriya daga kasar Faransa. Rahoton PUNCH

Tinubu ya bayyana haka a shafin na sa Tuwita, da Instagram a cikin jirgin sama ya rubuta “ hanyar zuwa gida”

Tinubu ya bar Najeriya ne jim kadan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar 27 ga watan Yuni kama kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta rawaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Gwamna Fayemi, Babajide Sanwolu da Rotimi Akeredolu sun kai wa Wike ziyara a Fatakwal

FARAN
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana hanyar dawo gida daga Faransa : FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, ya fitar a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani bangare sanarwar ta kara da cewa,

Ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da wasu muhimman taruka. Ana sa ran dan jam’iyyar APC zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.”

Wannan ci gaban dai ya biyo bayan kalaman Tinubu na cewa har yanzu yana neman abokin takararsa na zaben shugaban kasa a 2023.

Gwamnonin APC guda uku sun gana da Nyesome Wike a Fatakwal

Jihar Ribas - Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress guda uku a ranar Juma’a sun isa gidan gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers don wata ganawar sirri da za suyi dashi kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Gwamnonin sun hada da Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa