Jam'iyyar APC ta gamu babban tasgaro a Ribas, Wani jigo ya fice daga jam'iyyar

Jam'iyyar APC ta gamu babban tasgaro a Ribas, Wani jigo ya fice daga jam'iyyar

  • Shugaban kwamitin sulhu da zaman lafiya na jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyya
  • Dakta Dawari George, ɗan amutun tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sanar da haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban APC
  • Ya gode wa dukkan jagororin jam'iyyar da mambobinta bisa damar da suka ba shi ya yi wa ƙasa aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Jigon jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, wanda ya wakilci mazaɓar Asari-Toru da Akuku-Toru a majalisar tarayya daga 2011 zuwa 2015, Dr Dawari George, ya fice daga jam'iyyar.

PM News ta rahoto cewa kafin yanzu da ya ɗauki natakin murabus, Dawari George, shi ne shugaban kwamitin sulhu da zaman lafiya da APC ta kafa domin shawo kan rikicin da ya hanata sakat.

Dr Dawari George.
Jam'iyyar APC ta gamu babban tasgaro a Ribas, Wani jigo ya fice daga jam'iyyar Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Haka nan kuma ya kasance ɗan amutun tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ɗaya daga cikin jagororin APC a jihar ta Ribas, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Rikicin PDP ya tsananta, Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2023

Mista George ya kasance kwamishinan makamshi da Albarkatun ƙasa a gwamnatin Rotimi Amaechi, lokacin yana gwamnan jihar Ribas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bugu da ƙari yana ɗaya daga cikin yan takarar gwamnan, waɗan da suka hakura lokacin da jiga-jigan jam'iyyar su 19 suka zaɓi Tonye Cole a matsayin ɗan takarar maslaha na APC a zaɓen gwamnan Ribas 2019.

Meyasa jigon ya fice daga APC?

Murabus ɗin Mista George daga jam'iyyar na kunshe ne a wata wasika da ya aike wa shugaban APC na gunduma ta 1 (Ward 1), karamar hukumar Asari-Toru da ke jihar Ribas.

A wasikar, George ya rubuta cewa:

"Ina mai gode wa jagororin jam'iyya da baki ɗaya mambobi bisa damar da goyon bayan da suka ba ni na yi wa jiha da ƙasata aiki bakin kwarkwado a muƙaman da na rike lokacin ina jam'iyyar."
"A koda yaushe ina jin daɗin abokantaka da yan uwantakar da muka haɗa da juna a jam'iyya. Don Allah ka karɓi tabbaci na, ina muku fatan Alheri."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa APC ta shiga cikin ruɗani mai tsanani tsakanin 'ya'yanta bisa zargin ƙaƙaba Tonye Cole a matsayin ɗan takarar gwamna wanda aka ɗora wa Amaechi.

A wani labarin kuma Gwamnan Arewa ya dakatar ayarin motocinsa, ya taimaka wa wasu mutane da suka yi haɗari

Yayin da yake kan hanyar komawa gidan gwamnati daga Abuja, Gwamna Neja ya tsaya taimaka wa wasu motoci da suka yi haɗari a Paiko.

Gwamna Abubakar Sani Bello, ya jajantawa mutanen da ke cikin motocin tare da ɗaukar nauyin yi wa masu rauni magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262