Gwamnonin APC guda uku sun gana da Nyesome Wike a Fatakwal

Gwamnonin APC guda uku sun gana da Nyesome Wike a Fatakwal

  • Gwamna Fayemi na jihar Ekiti, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo sun kaiwa Nyesom Wike Ziyara a Fatakwal
  • Ana kyautata zaton ziyarar gwamnonin APC zuwa wajen Wike yana da nasabe da zaben shugabankasa mai zuwa
  • Gwamna Wike ya na fushi da jam'iyyar Peoples DemocraticParty PDP tun da ta fasa bashi tikitin takarar mataimakin shugaban kasa

Jihar Ribas - Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress guda uku a ranar Juma’a sun isa gidan gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers don wata ganawar sirri da za suyi dashi kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Gwamnonin sun hada da Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Har yanzu dai ba a san cikakken bayanin ganawar sirrin ba amma mai yiwuwa ba a rasa nasaba da zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Kungiyar TAM ta nesantar da Atiku daga rikicin bangarancin PDP a jihar Ekiti

Apc gov
Gwamnonin APC guda uku za su gana da Nyesome Wike a Fatakwal : Channels Television
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

apc gov
Gwamnonin APC guda uku za su gana da Nyesome Wike a Fatakwal : FOTO Channels Television
Asali: UGC

apc gov
Gwamnonin APC guda uku za su gana da Nyesome Wike a Fatakwal : FOTO Channels Television
Asali: UGC

Wike, jigo a jam’iyyar PDP, ana sa ran zai marawa dan takarar jam’iyyarsa, Atiku Abubakar baya, sai dai hasashe ya bayyana cewa gwamnan jihar Ribas bai ji dadi ba bayan an fasa ba shi tikitin mataimakin shugaban kasa. Rahoton Channels Televison

An ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Wike a Faransa a makon da ya gabata amma ofishin yada labaran Tinubu ta karyata labarin haduwar su

Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, Ndume

A wani labari, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Ali Ndume, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar. Rahoton Premium Times

Mista Ndume, dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar Borno ta Kudu, dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa na ga ‘yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa