Da Dumi-Ɗumi: Ɗan takarar shugaban ƙasa na LB ya bayyana mataimakinsa a 2023
- Bayan dogon lokaci da jita-jita, Peter Obi ya sanar da Datti Baba-Ahmed a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2023
- Ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar Labour Party ya ce a halin yazun sun gama shirin kwato Najeriya
- Ya kuma nemi afuwan masoya da magoya baya bisa ɗage ayyana mataimakin daga ranar Alhamis zuwa Jumu'a
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya bayyana, Datti Baba Ahmed, a matsayin wanda ya zaɓa ya zama abokin takararsa a zaɓen 2023.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bayyana Baba-Ahmed, wanda ya kafa jami'ar Baze, Abuja, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a Abuja yau Jumu'a.
Ɗan kimanin shekara 46 a duniya, tsohon Sanata ne mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta arewa a majalisar dattawan Najeriya.
Sanarwan ɗan takarar mataimakin ya zo ne awanni 24 bayan Daraktan ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Obi, Doyin Okupe, ya sanar da janye wa daga matsayin ɗan takarar mataimakin riko na jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wurin taron da aka shirya na musamman, Obi, ya nemi afuwar magoya bayansa bisa matakin ɗage sanarwan daga ranar Alhamis zuw ayau Jumu'a 8 ga watan Yuli.
Meyasa ya zaɓi Baba-Ahmed?
Peter Obi, ya ce a halin yanzu, ayyana mataimakin babbar alama ce da ke nun jam'iyya ta kammala shirin, 'dawo da Najeriya kan turba.'
A jawabinsa ya ce:
"A yau ina alfahari da cewa na cika buri da zakulo wani mutum wanda cancantar sa ta kai ƙololuwa kuma ya dace da zama kan kujerar mataimakin shugaban kasar Najeriya."
"Na san wasu za su ce ai bamu kai ga cin zaɓe ba a yanzu, amma zan iya faɗa muku da kwarin guiwa ta, na san inda muka dosa. Wannan haƙƙin mu ne mu gyara, hada kai da haɓaka Najeriya."
"Sai dai ba zamu kai ga haka ba sai mun jawo mutane da suke da tunani da manufa irin namu kuma suka shirya, saboda haka a yau ina mai jin alfaharin gabatar muku da zaɓin Allah, mataimakin shugaban kasa na gaba, Sanata Yusuf Baba-Ahmed."
Rahoton da Vanguard ta fitar a ya bayyana cewa tun Alhamis aka yi nufin za a kaddamar da Yusuf Datti Baba-Ahmed, amma sai hakan bai yiwu ba.
A wani labarin kuma hukumar kula da maniyyatan Najeriya NAHCON ta nemi afuwar maniyyatan da ta gaza cika wa burinsu na sauke farali a 2022
Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa ta nemi afuwar maniyyata 1500 da ta gaza kai su aikin Hajjin bana 2022.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Jumu'a, NAHCON ta ce zata maida wa kowa kuɗinsa ba tare da sisi sun yi ciwo ba.
Asali: Legit.ng