Da Ɗumi-Ɗumi: Maniyyata 1500 muka gaza kaiwa aikin Hajji, zamu biyasu kuɗaɗen su, NAHCON

Da Ɗumi-Ɗumi: Maniyyata 1500 muka gaza kaiwa aikin Hajji, zamu biyasu kuɗaɗen su, NAHCON

  • Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa ta nemi afuwar maniyyata 1500 da ta gaza kai su aikin Hajjin bana 2022
  • A wata sanarwa da ta fitar ranar Jumu'a, NAHCON ta ce zata maida wa kowa kuɗinsa ba tare da sisi sun yi ciwo ba
  • Ta sha alwashin cewa zata yi duk me yuwuwa don tabbatar da ba'a sake maimaita irin matsalar da aka samu ba

Abuja - Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa NAHCON, ta bayyana adadin maniyyata da ta gaza kai wa aikin Hajjin bana 1443/2022 kuma ta ce zata maida musu kuɗaɗen su cas.

A wata sanarwa da NAHCON ta fitar a shafinta na Facebook, hukumar ta yi dana sani tare da neman afuwar baki ɗaya maniyyatan Hajji 2022 bisa wahalhalun da suka sha da kunyar da ta basu yayin jigila zuwa ƙasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON.
Da Ɗumi-Ɗumi: Maniyyata 1500 muka gaza kaiwa aikin Hajji, zamu biyasu kuɗaɗen su, NAHCON Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

NAHCON ta kuma nemi afuwar gwamnatin tarayya, hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, matafiya masu zaman kansu, da ɗaukacin yan Najeriya bisa duk wani hali da suka tsinci kan su yan makonnin da suka shuɗe.

Sanarwan ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Abun takaici duk namijin kokarin kwashe baki ɗaya maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali a 2022, NAHCON ta gaza sauke nauyin da ke kanta baki ɗaya."
"Hakan ta faru ne sakamakon matsalolin da suka kunno kai ba zato a daƙiƙar ƙarshe ta jirkita duk tsarin mu na kammala jigilar maniyyata kamin ranar 27 ga watan Yuni, 2022."

Yawan maniyyatan da muka gaza kaiwa Hajji - NAHCON

Hukumar ta kuma bayyana adadin maniyyatan kowace jiha da ta gaza kai wa Hajjin bana kafin rufe filin saukar jiragen sama na Jiddah.

Maniyyatan sune; maniyyata tara daga jihar Bauchi, 91 daga jihar Filato, 700 daga jihar Kano da kuma ƙiyasin aƙalla maniyyata 750 daga ɓangaren kamfanonin yawon buɗe ido masu zaman kan su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya dakatar ayarin motocinsa, ya taimaka wa wasu mutane da suka yi haɗari

Hukumar ta ba da tabbacin cewa zata maida wa kowane maniyyaci da lamarin ya shafa kuɗaɗen sa cas yayin da zata maida hankali wajen inganta aikinta da magance kasawa nan gaba.

"NAHCON ta ɗauki darussa da dama kuma ba zata bari a maimaita wannan abun kunyar ba nan gaba, mun san ba bu wata magiyar ba da hakuri da zata share ɗacin da wasu Musulmai ke ciki sakamakon abinda ya faru."

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin da Talata, 11 da 12 ga watan Yuli, 2022 a matsayin na hutun shagalim babbar Sallah.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya taya ɗaukacin Musulman Najeriya murnar zagayowar wannan rana.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel