Jam’iyyar NNPP da Kwankwaso sun gamu da cikas a hanya daga bangaren Shekarau
- An samu wasu magoya bayan Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau da suka cije a Jam’iyyar APC
- Duk da Malam Ibrahim Shekarau ya shiga NNPP, wadannan magoya baya sun ce sam ba za su fice daga APC ba
- An yi wani taro da magoya bayan tsohon Gwamnan a Bichi a karkashin jagorancin Kwamred Bello Gadanya
Kano - Wasu magoya bayan Malam Ibrahim Shekarau da ake sa su a jerin ‘yan APC da suka shiga jam’iyyar NNPP sun zo da sabon labari a siyasar Kano.
Daily Trust ta rahoto wadannan mutane a ranar Lahadi su na cewa ba su sauya-sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa NNPP mai kayan dadi ba.
Shugaban wannan tafiya, Kwamred Bello Gadanya ya bayyana haka a wajen wani taron magoya bayan Ibrahim Shekarau da aka gudanar a garin Bichi.
Magoya bayan tsohon gwamnan sun shirya taron da ya tattara mabiya daga Arewacin jihar Kano.
Makasudin taron shi ne jaddadawa Duniya sun gamsu da wakilcin Sanata Barau Ibrahim Jibrin da ‘dan majalisar tarayya, Hon. Abubakar Kabir Abubakar.
Jaridar ta rahoto Kwamred Bello Gadanya yana cewa sun zabi su cigaba da zama a jam’iyyar APC mai mulkin Kano, sun yi watsi da batun rungumar NNPP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Har ila yau Gadanya ya ce sun yi tunani kafin cin ma wannan matsaya, kuma za su cigaba da mutunta juna duk da an samu bambancin siyasa tsakeninsu.
Shugaban karamar hukumar Bichi, Abdu Ara Bichi ya yi kira ga magoya bayan na Sanatan jihar Kano ta tsakiya da su yi zamansu a jam’iyyar APC a Kano.
Abdu Ara Bichi ya nemi wadannan ‘yan siyasa su tsaya a APC domin yi wa jam’iyyar aiki da nufin ta lashe zaben jiha da na shugaban kasa a shekarar badi.
Shekarau ya bar APC
Kafin Sanata Shekarau ya bada sanarwar ficewa daga jam’iyyar APC, sai da ya dauki lokaci yana tattaunawa da magoya bayansa a karkashin majalisar Shura.
A karshe kusan duka wadanda ke tare da Shekarau suka ce a bar APC, mafi yawa suka bada shawarar a shiga NNPP, wasu su ka bar zabi ga ubangidansu.
Kamar yadda ‘dan siyasar ya fada da bakinsa, hakan aka yi har suka yi watsi da jam’iyyar APC. Sai ga shi yanzu ana samun labari wasunsu sun dawo baya.
Tinubu ya dauki Malami
Ku na da labari cewa wasu matasa sun ba ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu shawarar wanda ya dace ya zama Mataimakinsa a zaben shugaban kasa
North East All Progressive Congress Enlightenment Circle ta yi watsi da su Kashim Shettima da sauran Gwamnoni, ta kawo shawarar a dauki Abubakar Malami.
Asali: Legit.ng