Wani Fasto ya fadawa mutane wanda za su zaba tsakanin Tinubu, Atiku da Obi a 2023
- Bishof Paulinus Ezeokafor ya gabatar da jawabi na musamman a cocin Madonna da ke garin Angulu
- Paulinus Ezeokafor wanda yana cikin manyan Limaman Katolika a Anambra ya tabo batun 2023
- Faston ya bada shawarar a zabi Peter Obi a 2023, ya ce ‘dan takaran ya fi kowa dacewa da mulki
Anambra - Babban limamin Kiristocin katolika Bishof Paulinus Ezeokafor ya fito yana kira ga al’umma su yi tunanin makomar Najeriya wajen zabe.
Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa Bishof Paulinus Ezeokafor ya fadawa mutane su ajiye batun kabilanci da addini a wajen zaben shugaban kasa.
Babban Faston yake cewa a sanin da ya yi wa Peter Obi, ya fi kowa cacantar zama shugaban kasa.
A cewar Ezeokafor, Peter Obi mutum ne mai daraja, mai tsantseni wajen kashe dukiya da saukin kai, sannan ya yi abin-a-yaba da yake mulki a Anambra.
Tsakanin 2006 da shekarar 2007 zuwa 2014, Peter Obi ya rike kujerar gwamnan Anambra a jam’iyyar APGA. Daga baya ya koma, PDP yanzu ya na LP.
Faston da ake ji da shi a garin Awka yake cewa a duk cikin masu takarar shugaban kasa, babu wanda Najeriya ta ke bukata a halin yanzu irin Mista Obi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ranar Sikila ta Duniya
Rahoton yake cewa Faston duk ya yi wannan jawabi ne a wajen taron da aka shirya na ranar masu cutar sikila ta Duniya da aka yi ranar Lahadin da ta wuce.
A wajen taron, an yabi Peter Obi domin kwanakin baya ya bada gudumuwar Naira miliyan 2 wanda da su ne ake daukar dawainiyar wasu masu cutar sikila.
A tanadi PVC - Ezeokafor
Baya ga bada shawarar a zabi ‘dan takaran na jam’iyyar LP, da yake huduba a cocin ‘yan katolika na garin Agulu, Faston ya bada shawarar a yi tanadin PVC.
Malamin addinin ya bukaci duk wani wanda ya isa shekara 18 da bai da katin zabe, ya yi maza ya yi rajista da hukumar INEC domin ya kada kuri’arsa a 2023.
Haka zalika, Faston ya jawo hankalin mabiyansa a kan bautar Ubangiji domin samun rahama. A game da batun sikila, yace a rika yin gwaji tun kafin ayi aure.
Peter Obi zai dawo NNPP?
Ku na da labari takarar Obi za ta fuskanci barazana daga Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP, Bola Tinubu a APC, da irinsu Rabiu Kwankwaso da ya tsaya a NNPP.
Ana da labari cewa shi ma Peter Obi ya gabatar da wani jawabi a taron da cocin RHOGIC suka shirya a Abuja, a nan ya tabbatar da cewa su na magana da NNPP.
Asali: Legit.ng