Abu ɗaya zai ceci APC ba zata sha kaye a zaɓen 2023 ba, Sanata Adamu
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya ce tare da goyon bayan da jam'iyya me mulki ke samu ba zata sha ƙasa a zaɓen 2023 ba
- Adamu ya ce jam'iyyar APC ta na da goyon bayan yan Najeriya miliyan 43 bisa haka ita ke da nasara matukar sahihin zaɓe aka yi
- Ya ƙara da cewa APC ta buɗe kofa ga kowa, ta yadda aka samu mace yar takarar gwamna a arewacin Najeriya
Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yaƙininsa cewa jam'iyya mai mulki zata lashe zaɓen 2023 matuƙar sahihin zaɓen aka gudanar.
Adamu ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin jakadar Poland a Najeriya, Joanna Tarnawska a ofishinsa ranar Laraba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Adamu ya ce, "Tare da ɗumbin goyon bayan da jam'iyyar ke samu daga yan Najeriya miliyan 43m, ba bu ta yadda zata faɗi zaɓen 2023."
"Jam'iyyar APC ta san abin da zai biyo bayan samun cigaba a Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar Afirka kuma mun shirya sadaukar da kan mu a zaɓen dake tafe kamar yadda muke gani a sauran ƙasashe."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Najeriya ƙasa ce mai tasowa a cigaban demokaraɗiyya kuma tana ɗaukar darasi a matakan gudanar da zaɓe, amma APC zata cigaba da yin duk me yuwuwa don demokaraɗiyya ta ƙara samun gindin zama a Najeriya."
Adamu ya sanar da jakadan Poland ɗin cewa, sakamakon damar da APC ke ba kowa, an samu mace da ta lashe zaɓen takarar gwamnan a jihar arewacin Najeriya.
Muna kira aƙara ba mata da matasa dama
Jakadar, wacce ta ziyarci Adamu a karon farko tun bayan babban taron APC na ƙasa, ta taya shi murnar zama ciyaman ɗin APC.
Ta bayyana cewa ƙasarta na sha'awar ganin an samu cigaba ta ɓangaren siyasa a Najeriya kuma tana fatan ganin an mika mulki hannun sabon shugaba lami lafiya bayan ƙarewar wa'adin shugaba Buhari a shekara mai zuwa.
Tarnawska ta buƙaci APC ta sama wa mata da matasa damarmaki don su fito su ba da tasu gudummuwar wajen cigaban siyasar ƙasa.
A wani labarin kuma Magana ta ƙare, Atiku Abubakar ya zaɓi wanda yake so ya zama mataimakinsa a 2023
Bayan dogon lokaci ana kace nace, wasu bayanai sun tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya zaɓi wanda ya ke so ya zama abokin takararsa.
Jam'iyyar PDP ta tsinci kanta cikin ƙaƙanikayi game da wanda zai zama mataimaki, sai dai Gwamna Wike da Okowa ne a sahun gaba.
Asali: Legit.ng