Gwamna Okowa ya cancanci zama mataimakin Atiku, PDP ta fitar da sakamakon tantancewa

Gwamna Okowa ya cancanci zama mataimakin Atiku, PDP ta fitar da sakamakon tantancewa

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa gwamna Okowa ya dace da zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa don bata gano wani aibu ba
  • Kwamitin tantancewa ya ce gwamnan na jihar Delta yana da kwarewa sakamakon ya rike muƙamai da dama a jiharsa
  • A yau Alhamis, Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ya sanar da sunan Okowa a matsayin wanda ya zaɓa

Abuja - Kwamitin tantance ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP ya sanar da cewa ya gano gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya cancanci zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaɓen 2023.

Shugaban kwamitin, Chief Tom Ikimi, ya bayanna haka ga manema labarai a Abuja bayan jam'iyya ta gabatar da Okowa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Atiku tare da gwamna Okowa.
Gwamna Okowa ya cancanci zama mataimakin Atiku, PDP ta fitar da sakamakon tantancewa Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Ikimi ya ce aikin kwanitinsa shi ne tantance wanda aka zaɓa ya zama abokin takara don tabbatar da cewa jam'iyya ba ta jawo wa kanta wata matsala ba.

Shugaban kwamitin ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Okowa ya rike muƙamai da dama a jihar Delta da yankunan kananan hukumomi, ya rike kwamishina kuma ya wakilci wata mazaɓa daga jihar a majalisar dattawan Najeriya."
"Aikin kwamitin mu shi ne tabbatar da sahihancin cancantarsa sabosa bamu fatan nan gaba muje Kotu bayan zaɓe yayin da mutane zasu fara kalubalantantar wanda ya cancanta da wanda be cancanta ba."
"Kwamitin mu ya gano cewa ya na da cikakkiyar cancanta, yana da lafiya kuma ga saukin kai, sannan a shirye yake ya jawo duk waɗan da suka so matsayin don samun zaman lafiya a cikin jam'iyya."

Sauran mambobin kwamitin da ya tantance Okowa

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Atiku Abubakar ya zaɓi wanda yake so ya zama mataimakinsa a 2023

Mambobin kwamitin da PDP ta kafa don aikin sun haɗa da Akilu Indabawa, a matsayin Sakatare da Mista Sunday Omobo.

Sauran sune; Idris Wada, Chief Osita Chidoka, Binta Bello, Chief Mutiat Adedoja, Austin Opara, Farfesa Aisha Madawaki, Misis Ayotunde George-Ologun, Chief Chidiebelu Mofus da kuma Fidelis Tapgun.

A wani labarin kuma Bola Tinubu ya gaje babban ofishin yaƙin neman zaben Buhari a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki, Bola Tinubu, ya samu ofishin yaƙin neman zaɓe na biyu tun bayan nasararsa.

An bai wa ɗan takaran ofishin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi amfani da shi yayin Kanfe a zaɓen 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262