Tsohon kwamishina da wasu ɗaruruwan mambobin APC makusantan Ministan Buhari sun koma PDP
- Yayin da kowace jam'iyya ke shirin tunkarar zaɓen gwamnan Osun a wata mai kamawa, APC ta rasa wasu manyan jigoginta
- Tsohon kwamishina da wasu mambobin APC magoya bayan Rauf Aregbesola, ministan cikin gida sun sauya sheƙa zuwa PDP
- Sai dai mai magana da yawun APC a jihar ya ce dukkan masu sauya shekan ba su da amfani a jam'iyya
Osun - Dandazon mambobin APC waɗan da ke goyon bayan tsohon gwamnan jigar Osun kuma Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, sun sauya sheka zuwa PDP ranar Laraba.
Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin naɗin sarauta lokacin mulkin Aregbesola, Kolapo Alimi, shi ya jagoranci ɗaruruwan mambobin daga kananan hukumomi 16 zuwa PDP.
Hakan ya biyo bayan rikicin da yaƙi ci ya ƙi cinyewa a jam'iyyar APC reshen jihar Osun sanadiyyar rashin jituwa tsakanin Aregbesola da gwamna mai ci, Adegboyega Oyetola.
Shugabannin PDP da ɗan takarar gwamnan a zaɓen da ke tafe ranar 16 ga watan Yuli a jihar, Ademola Adeleke, sune suka tarbi masu sauya shekan a Sakatariyar PDP da ke Osogbo, babban birnin Osun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa suka zaɓi komawa PDP?
Mista Alimi, wanda ya jagoranci masu sauya sheƙar, ya ce sun shirya aiki tare da da jam'iyyar PDP domin kayar da gwamna Oyetola a zaɓe mai zuwa.
Ya ce:
"Jim kaɗan bayan rantsar da gwamna Oyetola ya fara raba kai da yaƙar masoyan minista Aregbesola. Mun kai koken mu ga masu ruwa da tsaki amma ba wani abu da aka yi."
"Kun sani cewa Aregbesola babban ƙusa ne a APC ba zai iya barinta ba amma a wurin mu ba zamu cigaba da zama wurin da ake cutar da mu ba, ya kamata mu matsa."
Bayan sauya sheka zuwa APC, Kujerar mataimakin gwamnan PDP ta fara tangal-tangal, Majalisa zata tsige shi
Tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar PDP ta ƙasa, Prince Diran Odeyemi, ya ce wannan cigaban wata alama ce ta nasarar Adeleke a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Ya APC suka ji da wannan batu ana gab da zaɓe?
Amma kakakin jam'iyyar APC reshen Osun, Mista Kunle Oyatomi, ya ce dama can Alimi da yan tawagarsa ɓarna kawai suke wa jam'iyya kafin ficewarsu don haka ba za'a yi rashin su ba.
A wani labarin kuma Magana ta ƙare, Atiku Abubakar ya zaɓi wanda yake so ya zama mataimakinsa a 2023
Bayan dogon lokaci ana kace nace, wasu bayanai sun tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya zaɓi wanda ya ke so ya zama abokin takararsa.
Jam'iyyar PDP ta tsinci kanta cikin ƙaƙanikayi game da wanda zai zama mataimaki, sai dai Gwamna Wike da Okowa ne a sahun gaba.
Asali: Legit.ng