Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

  • Atiku Abubakar, 'dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP ya zabi Gwamna Okowa a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa
  • Atiku ya bayyana Okowa a matsayin mayaki mai nagarta wanda ya mallaki halayen da shugaban kasa zai mallaka a fannin mulki
  • Atiku ya ce dole ne abokin tafiyarsa ya fahimci halin da tsaro, tattalin aziki, cigaban kasa, ilimi da mtasan kasar nan ke ciki

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma 'dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya darzo gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin tafiyarsa a zaben da za a yi shekara mai zuwa.

Atiku ya zabi Okowa ana gobe wa'adin da INEC ta bayar na mika sunan mataimakin 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyun siyasa zai cika.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

A yayin jawabi a taron, Atiku ya ce yanke hukunci tare da zabo mutum daya daga cikin mutane ukun da aka bukata abu ne matukar wahala.

Atiku Abubakar tare da Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta
Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar. Hoto daga Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya kwatanta Okowa da mayaki wanda ya kware a fannin siyasa kuma wanda ya yi sunan arziki a jiharsa, Delta tare da jam'iyyar PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Atiku:

"Na dinga tuntube-tuntube da masu ruwa da tsaki daban-daban a jam'iyyar mu da suka hada da gwamnoni, NWC, kwamitin yaraddu da sauran shugabanni domin neman hikimarsu da taimakonsu.
"A yayin wannan neman shawarar ne na gane cewa, wanda za mu yi tafiyar nan dole ne ya kasance yana da karfin da zai gaje ni, wato shugaban kasa na gaba.
“A takaice dai, dole ne ya kasance yana da nagartar zama shugaban kasa. Dole ya kasance yana da sani matuka kan kasarmu da halin da muguwar gwamnatin APC suka saka mu, ya fahimci halin matsin da jama'a da yawa na kasar nan ke fuskanta, ya fahimci muhimman tsarikan farfado da tattalin arziki da cigaban matasa.

Kara karanta wannan

Muna bukatar PDP ta koma mulki a 2023: Abokin tafiyar Atiku ya lashi takobi

"Dole ne mutumin ya gane miuhimmancin ilimi a cigaban al'umma ta yadda za mu shirya matasa domin gogayya da sabbin salon da duniya ke tahowa da su.
"Abokin tafiyata dole ne ya fahimci cewa ba tare da tsaro ba, cigaba zai yi matukar wahala saboda masu saka hannayen jari na gida da ketare za su tsere, ba za su dawo su zuba hannayen jari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng