Muna bukatar PDP ta koma mulki a 2023: Abokin tafiyar Atiku ya lashi takobi
- Gwamna Ifeanyi Okowa yace yan Najeriya na bukatar jam'iyyar PDP ta koma bakin mulki a 2023
- Alhaji Atiku Abubakar ya zabi Okowa matsayin abokin tafiyarsa a zaben shugaban kasar 2023
- Yanzu jamiyyar APC da Asiwaju Bola Tinubu ake jira su zabi wanda zai zama mataimakin shugaba
Abuja - Farawa da iyawa, Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa ko ta kaka sai jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Okowa, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan alantasa matsayin abokin tafiyar dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin PDP, Alhaji Atiku Abubakar, rahoton AriseTV.
Okowa yace:
"Ina godewa Allah cewa cikin takwarori na an zabe ni yau matsayin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar."
"Akwai babban aiki gabanmu, kuma zamuyi iyakan kokarinmu wajen tabbatar da jam'iyyar ta yi nasara."
"Wajibi ne mu baiwa shugabanmu goyon baya. Akwai bukatar mu bada hadin kai a gundumominmu, kananan hukumominmu da jihohinmu. Akwai bukatar PDP ta koma mulki."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa
Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai gabatowa.
Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP a ranar Laraba ya zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin 'dan takarar shugabancin kasan.
Mambobin NWC sun yi zabe inda Wike ya samu kuri'u 13 yayin da Okowa ya samu uku kacal, lamarin da yasa masu ruwa da tsakin suka aminta da Wike.
Sai dai, Atiku Abubkar na gano ya kasa sakin jiki da Wike a matsayin abokin tafiyarsa sabodaya sakankance cewa gwamnan baya kaunarsa.
Asali: Legit.ng