Magana ta kare, watakila a tantance Gwamnan PDP a matsayin Abokin takarar Atiku a 2023
- Kwamitin Jam’iyyar PDP zai tantance wanda zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa
- Jam’iyyar PDP ta tsaida Alhamis ne a matsayin ranar da kwamitin da aka kafa zai yi wannan aiki
- Debo Ologunagba ya ce Tom Ikimi ne zai yi wannan aiki tare da wasu kusoshin jam’iyyar adawar
Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta kafa wani kwamiti na musamman da zai tantance mata ‘dan takarar kujerar mataimakin shuganan kasa a 2023.
Rahoto ya fito daga Daily Trust cewa Gwamna Nyesom Wike shi ne zabin da jam’iyyar ta yi. Sai dai har yanzu PDP ba ta fito an sanar da Duniya hakan ba.
A wani jawabi da sakataren yada labarai na PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar, ya yi maganar tantance wanda zai tsaya takarar mataimakin shugaban kasa.
Mista Debo Ologunagba ya ce bangare na VI a sakin layi na 14 na dokar zaben jam’iyyar PDP ya yi bayanin kafa kwamitin da zai tantace ‘dan takaran na su.
Jawabin da Ologunagba ya fitar a ranar Talata ya nuna ‘yan majalisar NWC sun amince da wadanda za su zauna a kwamitin da zai yi aikin tantancewar.
Wannan kwamiti ne zai tantance ya kuma tabbatar da abokin takarar Atiku Abubakar a zaben 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Su wanene 'yan kwamitin?
Kamar yadda ya shaidawa manema labarai, Kakakin na PDP ya ce Cif Tom Ikimi zai jagoranci aikin kwamitin a ranar Alhamis a sakatariyar jam’iyyar a Abuja.
Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Kyaftin Idris Wada, Osita Chidoka, Rt. Hon. Binta Bello, Rt. Hon. Austin Opara, Farfesa Aisha Madawaki sai Fidelis Tapgun.
Atiku ya canza tsari a 2023
A wani rahoton, an ji shugaban PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu yana umartar ‘yan jam’iyyar su karkare maganar ‘dan takara daga Laraba zuwa ranar Juma’a.
Iyorchia Ayu ya ce a wannan karo Atiku ya bukaci jam’iyya ta zaba masa wanda ya kamata ya zama abokin takararsa, akasin yadda ya yi lokacin zaben 2019.
Iwhnurohna Monitoring Group
Labarin da mu ka samu daga Premium Times ya nuna ‘yan kungiyar IMG ta mutanen Neja Delta da ke zama a Turai da Amurka su na goyon-bayan Nyesom Wike.
Kakakin kungiyar, Chindah Wami ya roki alfarma wajen Atiku Abubakar da ya zabi Wike ya zama masa mataimaki domin PDP ta kai ga nasara a zabe mai zuwa.
Dazu an ji labari cewa a karshe da aka je aka dawo, Kwamitin da Jam’iyyar PDP ta kafa ya zakulo babban abokin adawar Atiku Abubakar ne a zaben tsaida gwani.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘Yan kwamitin na Janar Aliyu Gusau sun fi natsuwa da Gwamnan jihar Ribas a kan Gwamnonin jihohi ukun da aka yi la’akari da su.
Asali: Legit.ng