Lawan ya Jajanta wa Kansa da Sauran Sanatocin da Aka Lallasa a Zaben Fidda Gwani

Lawan ya Jajanta wa Kansa da Sauran Sanatocin da Aka Lallasa a Zaben Fidda Gwani

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, ya taushi kansa da sauran 'yan majalisa da aka lallasa a zabukan fidda gwani
  • Lawan ya yi jawabi tare da kara wa abokan aikinsar karfin guiwa kan su mayar da hankali wurin duban tsaro da gyara dokokin zabe na kasar nan
  • Ya taya wadanda suka yi nasara murna tare da musu fatan nasara a zabukan gaba, ya yi fatan komai ya daidaita garesu cikin gajeren lokaci

FCT, Abuja- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya jajanta wa abokan aikinsa da suka kasa samun tikitin takara a karkashin jam'iyyun su a zaben 2023 mai zuwa.

Lawan ya sanar da hakan ne yayin da aka dawo zaman majalisar a ranar Talata a jawabinsa na maraba da 'yan majalisar daga hutun da suka yi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

Majalisar dattawan ta dakatar da zamanta a ranar Laraba, 11 ga watan Mayun 2022 domin bai wa 'yan majalisar damar shiga su yi zabukan fidda gwani na jam'iyyunsu.

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, Yayin Zamana Majalisa
Lawan ya Jajanta wa Kansa da Sauran Sanatocin da Aka Lallasa a Zaben Fidda Gwani. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Lawan, wanda ya nemi tikitin takarar shugabancin kasa da kuma sama da 'yan majalisar 20 da aka lallasa a zabukan fidda gwanin da aka yi a fadin kasar nan tsakanin watan Mayu da Yuni duk sun dawo majalisar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban majalisar dattawan ya yi kira ga sanatocin da aka lallasa a zabukan da kada su sare, su mayar da hankali kan lamurran tsarikan siyasa na jam'iyyun su tare da manta sakamakon zabukan fidda gwanin ba.

Lawan ya ce akwai bukatar majalisar ta fifita batun kalubalen tsaron kasar nan kuma ta kara duba gyararrun dokokin zabe.

Ya ce yadda aka kammala zabukan fidda gwanin da tsarikansu ya bayyana lamurran da sai an tsaya an duba su a majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

A yayin jawabi kan sakamakon zabukan fidda gwanin, ya ce, "wasu daga cikinmu sun nemi tikitin sanatoci, wasu abokan aikinmu sun nemi na gwamnonin jihohinsu kuma hudu daga cikinmu sun nemi shugabancin kasa.
"Mun fuskanci sakamako daban-daban, amma a matsayin mu na 'yan siyasa, tsugune bata kare ba.
"Mu cigaba da goyon bayan tsarikan siyasa da muka yarda da su. Abokan aikinmu da suka samu nasara, muna muku fatan nasara a zabukan gaba. Sai wadanda ba su samu nasara ba, muna fatan daga yanzu zuwa wani lokaci komai zai daidaita."

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

A wani labari na daban, Duka biyu kenan ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan. 'Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC kuma wanda ya ci zaben fidda gwani, Bashir Machina, ya ki janyewa Lawan.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwani: Yadda wasu 'Yan takaran APC suka kamu gaibu, suka sha kashi a hannun Bola Tinubu

Lawan, wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa, ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar shugabancin kasa da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.

Da farko an fara bayyana shugaban majalisar dattawan a matsayin 'dan takarar yarjejeniya na jam'iyyar, amma gwamnoni 13 na arewacin Najeriya sun yi watsi da lamarin inda suka ce ya zama dole a mika mulki kudancin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng