Atiku yana maganar saida wuta, matatun mai da jirgin kasan Najeriya idan ya karbi mulki

Atiku yana maganar saida wuta, matatun mai da jirgin kasan Najeriya idan ya karbi mulki

  • Alhaji Atiku Abubakar bai goyon bayan gwamnati ta rika kula da kadarorin da ke jawo mata asara
  • Atiku Abubakar ya sha alwashi idan ya karbi shugabanci, zai saidawa ‘yan kasuwa matatun danyen mai
  • ‘Dan takarar ya nuna zai saida kamfanin TCN da kamfanin jiragen kasan Najeriya ga ‘yan kasuwa

Abuja - Atiku Abubakar wanda shi ne zai yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a 2023 zai karfafa ‘yan kasuwa, ya ragewa gwamnati karfi.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni 2022 cewa Atiku Abubakar ya fitar da jerin manufofinsa na saida kadarorin gwamnati.

Idan ‘dan takarar ya yi nasarar zama shugaban Najeriya, ya ci burin saida matatun danyen man kasar nan a kasuwa domin a bunkasa harkar mai.

Kara karanta wannan

Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar

Haka zalika mulkin Atiku Abubakar zai kawo karshen mallakar TCN da gwamnatin tarayya ta ke yi, zai saida kamfanin lantarkin ne ga ‘yan kasuwa.

Rahoton yace ‘dan siyasar zai saida jiragen kasan Najeriya da wasu abubuwan more rayuwa ga ‘yan kasuwa domin gwamnati ta daina tafka asara.

Da yake dogon bayani a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ‘dan takarar yace manufofin tattalin arzikinsa za su taimaka wajen bunkasa kasuwanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku's bid
Atiku Abubakar tare da wasu jagororin PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Har ila yau, Atiku ya ce tsare-tsaren da zai kawo, za su yi sanadiyyar samar da ayyukan yi a kasa.

Manufofi uku na Atiku

Yadda ‘dan siyasar zai yi wannan kuwa shi ne ta hanyoyi uku. Na farko, zai ba ‘yan kasuwa damar kawo cigaba, watau gwamnati za ta cire hannuwanta.

Sannan idan mulki ya fada hannun PDP, za ayi kokarin ganin babu ruwan gwamnatin da kula da matatun danyen mai, da harkar wuta da jiragen kasa.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

Alkawarin da Atiku Abubakar ya yi shi ne zai ba ‘yan kasuwa damar da za su baja hajarsu wajen bunkasa bangarorin sufuri, wutar lantarki da kuma mai.

Abu na uku da ‘dan takaran zai yi shi ne a daina katsalanda, a bar farashi a hannun ‘yan kasuwa.

Atiku na lissafin doke APC

An samu labari ‘Dan takaran na PDP, Atiku Abubakar zai iya hada karfi da LP da Jam’iyya mai kayan marmari domin ya zama shugaban kasa a 2023.

A gefe guda, babban ciwon kan Bola Tinubu shi ne yadda zai dauko ‘dan takaran da zai samu karbuwa a zabe, kuma ya tafi da kowane bangaren kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng