Jerin sunayen manyan jiga-jigan APC da suka koma PDP bayan Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na jam'iyyar

Jerin sunayen manyan jiga-jigan APC da suka koma PDP bayan Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na jam'iyyar

A halin da ake ciki a yanzu, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na rasa karfinta a jihar Kebbi yayin da Peoples Democratic Party (PDP) ke kara karfi bayan wasu manyan jiga-jiganta guda takwas sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawar kasar.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa manyan jiga-jigan na APC a Kebbi sun sauya sheka ne bayan korafe-korafen cewa an yi kutse a tarukan jam’iyyar da aka gudanar a jihar.

Wadanda suka sauya shekar sune yan majalisa a majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin jiha.

Jerin sunayen manyan jiga-jigan APC da suka koma PDP bayan Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na jam'iyyar
Jerin sunayen manyan jiga-jigan APC da suka koma PDP bayan Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na jam'iyyar Hoto: Peoples Democratic Party
Asali: Facebook

Masu sauya shekar sune:

Majalisar dattawa

  1. Sanata Adamu Aliero (Kebbi ta tsakiya)
  2. Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta arewa)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar wakilai

  1. Honourable Mohammed Umar Jega (mai wakiltan mazabar Aliero/Jega/Gwandu a majalisar tarayya)
  2. Honourable Abdullahi Zumbo (mai wakiltan Dandi/Arewa a majalisar tarayya)

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

Majalisar dokokin jiha

  1. Habibu Labbo (mai wakiltan mazabar Gwandu)
  2. Ismaila Biu (mai wakiltan mazabar Arewa)
  3. Mohammed Aliero (mai wakiltan mazabar Aliero)

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

A gefe guda, ana tsaka da neman ganin waye dai zama mataimakin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai rike da tutar takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, mai bada shawara ta musamman ga Abdullahi Umar Ganduje a kafafan sada zumunci, Shehu Isa ya bayyana dalilan da yasa ya ke ganin ya kamata jam'iyyar da Tinubu su dauki Ganduje a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023.

Isa wanda ke kokarin ganin ya gamsar da cewa bai saba doka ba tikitin Musulmi da Musulmi, inda ya ce Ganduje ne yafi cancantar rike tutar takarar shugaban kasa a jam'iyyar baya ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng