2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

  • Daga yanzu zuwa ranar Juma’a, dole a san duka wadanda za su yi takarar shugaban kasa a 2023
  • Babu mamaki Bola Tinubu ba zai dauki Kirista ya yi masa takarar mataimakin shugaban kasa ba
  • Ana sa ran zuwa Litinin za a san wa PDP ta dauka tsakanin Gwamnonin Akwa Ibon, Delta da Ribas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Nan da ranar Juma’a dole kowace jam’iyyar siyasa za ta gabatarwa hukumar INEC sunayen ‘yan takararta a zaben shugaban kasa na 2023.

Punch ta kawo rahoto cewa mafi yawan jam’iyyun da za su shiga zaben 2023 su na kokarin ganin sun gama lissafinsu kafin wa’adin da aka bada ya kure.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta ce ba za ta kara lokacin gabatar mata da sunaye ba.

Matsayin Jam’iyyar PDP

A PDP, jam’iyya ta kafa wani kwamiti ne da zai yi aikin zakulowa Alhaji Atiku Abubakar wanda ya fi dacewa su yi takara tare a zabe mai zuwa na 2023.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

Wannan kwamiti zai yi zaman karshe a ranar Talata domin karkare magana a kan batun tikitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin yana kunshe da ‘yan majalisar NWC, tsofaffin gwamnoni, ‘yan majalisar amintattu da za su ga wa fi dacewa da takarar mataimakin shugaban kasa.

Bola Tinubu
'Dan takaran APC, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Takarar Musulmi da Musulmi?

Rahoton da aka fitar ya nuna jam’iyyar PDP da ‘dan takararta, Asiwaju Bola Tinubu, su na tunanin yin tikitin Musulmi da Musulumi ne a babban zaben 2023.

Jam’iyyar mai mulki ta gagara samun wani daga Kirista daga jihohin Arewa wanda zai iya taimakawa APC wajen tika Atiku Abubakar da PDP da kasa.

Wani babba a jam’iyyar ya shaidawa jariar cewa ana cigaba da zama domin ganin yadda za a bullowa lamarin, amma an fara tunanin dauko wani Musulmi.

Kamar yadda majiyar ta shaida, an ajiye batun Gwamnan Filato, Simon Lalong da SGF Boss Mustafa domin ganin ba su da nauyi sosai a mizanin siyasa.

Kara karanta wannan

Neman Mataimkin Atiku: PDP Ta Kafa Kwamiti A Yayin Da Wike Da Okowa Ke Neman Zama Mataimakin Shugaban Kasa

Wa zai yi takara a APC da PDP?

Mutane uku aka rahoto cewa daga cikinsu za a samu wanda zai nemi ya yi wa Atiku mataimaki.

Wadannan ‘yan siyasa uku su ne gwamnan Delta, Dr Ifeanyi Okowa, Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

APC kuwa ta na tunani ne tsakanin Sanata Kashim Shettima; Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamna Atiku Bagudu da kuma Gwamna Nasir El-Rufai.

PDP za ta hada-kai da LP, NNPP

A baya kun ji labari babban ciwon kan Bola Tinubu shi ne yadda zai dauko ‘dan takaran da zai samu karbuwa a zabe, kuma ya tafi da kowane bangare.

Watakila kuma ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar zai nemi hada karfi da LP da Jam’iyya mai kayan marmari domin ya zama shugaban kasa a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng