Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC
Bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), mai rike da tutar jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, yana kokarin ganin ya sasanta tsoffin yan takara wadanda suka fusata kan sakamakon zaben.
A cikin kasa da mako daya, Tinubu ya ziyarci akalla yan takara biyar wadanda suka nuna sha’awar darewa kujerar shugaban kasa a 2023 a karkashin inuwar APC.
Yawancin wadannan tsoffin yan takarar sun shiga jerin sunayen da gwamnonin APC suka shirya wanda aka sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zabi daya daga cikinsu.
Yan takarar sune:
1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Rotimi Amaechi
3. Gwamna Yahaya Bello
4. Gwamna Dave Umahi
5. Godswill Akpabio
6. Ibikunle Amosun
Atiku zai nemi hadin-kan Kwankwaso da Obi a 2023, APC na lissafin abokin takaran Tinubu
A wani labarin, ‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar ya na tunanin zama da Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a kan batun 2023.
Punch ta fitar da rahoto a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni 2022 da ya bayyana cewa PDP za ta iya hada-kai da wadannan ‘yan takara biyu na jam’iyyan adawa.
Peter Obi ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki da ya nemi takara a zaben 2019, a dalilin sabanin da ya samu da jagororin PDP ya sauya-sheka zuwa jam'iyyar LP.
Asali: Legit.ng